Masu Garkuwa Da Mutane
Miyagun ƴan bindiga sun buƙaci yan uwan da mutanen da suka sace a Gonin Gora su haɗa Naira tiriliyan 40 a matsayin kuɗin fansa da kuma motoci da babura.
Masu garkuwa da mutane da suka sace almajirai a jihar Sakkwato sun nemi a tattara musu Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa gabanin su sako su.
Yayin da 'yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare, Sheikh Ahmed Gumi ya shawarci Bola Tinubu kan sulhu sabanin kuskuren da aka yi a gwamnatin Muhammadu Buhari.
A jihar Kano, jami’an NSCDC sun damke ‘dan shekara 85 da zargin garkuwa da mutane. Idan dai gaskiya ne, da alamu tsufa tayi wa wannan mutumi gardama.
Tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki Anguwar Makera karkashin garin Kwasakwasa da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna tare da kashe masallata.
Matar shugaban kasa Oluremi Tinubu ta yi Allah wadai da ‘yan bindiga, ta bayyana su a matsayin matsora kuma ta nemi a dunga yanke hukuncin kisa a kansu.
Shugaban makarantar firamare ta LEA da ke Kuriga a jihar Kaduna, Sani Abdullahi ya tabbatar da cewa dalibai 287 na makarantar ne ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su.
Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta kama wani dattijo mai shekaru 85 mai suna Ibrahim Usman da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro dan shekara 3 a Kano.
Wasu da ake zaton 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ne sun farmaki makarantar firamare ta LEA a garin Kuriga, karamar hukumar Chikun ta Kaduna, sun sace dalibai.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari