
Manyan Labarai A Yau







An yi jana’izar Harira Jibril, mai cikin da kungiyar IPOB ta yi wa kisan gilla tare da ’ya’yanta hudu da dan cikinta a Jihar Anambra a safiyar ranar Laraba.

Dattijon da ya shafe tsawon shekaru 70 yana sallah a bayan limaman Masallacin Ka’aba, Sheikh Muhammad bin Abdul-Wahhab Aal Ash-Sheikh, ya rasu a yau Laraba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da kisan da ’yan haramtacciyar kungiyar ’yan awaren IPO ke yi a fadin yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin cocin kotolika da wasu mutane guda bakwai a kananan hukumomin Kafur da Safana da ke jihar Katsina.

Lamidon Adamawa, Mai martaba Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, ya bukaci al’ummar Musulmi da su ji tsoron Allah tare da tuna mutuwa a rayuwar su ta duniya.

Shehu Sani ya ce wani dan takarar kujerar majalisar tarayya a jihar Kaduna ya yi nasarar kwato kimanin naira miliyan 100 da ya baiwa deleget din jam’iyyar PDP.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari