Shafukan ra'ayi da sada zumunta
Sheikh Khalil ya ce babu wani dauri da za a yi wa Murja wanda zai kawo maslaha a abubuwan da take yi, inda ya roki Gwamna Abba da ya ba ta mukamin 'hadima'.
Wani magidanci ya samu kansa cikin halin dana sani bayan matarsa da ya kai Burtaniya ta ci amanarsa da tsohon saurayinta. Magaidancin ya kashe sama da N30m.
Mun duba shafin Abubakar na X (tsohon Twitter) amma ba mu sami labarin yana bayar da kyautar naira 100,000 ga ’yan Najeriya ba, kawai aikin 'yan damfara ne.
Elon Musk, mai kamfanin X ya yi martani bayan daukewar shafukan Facebook da Instagram inda ya ce su kam shafinsa na tafiya yadda ya kamata ba kamar na Zuckerberg ba.
Facebook, Messenger da Instagram na kamfanin Meta sun dauke a duk duniya, wanda ya bar dubban daruruwan masu amfani da su cikin yanayi na rashin abin yi.
Gwamnatin Najeriya ta ci Binance tarar $10b bayan kama kamfanin da aika laifukan da taimaka wajen faduwar darajar Naira tare da jawowa kasar asara mai yawa.
Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta hana Airtel, MTN da sauran kamfanonin sadarwa rufe layukan abokan huldar da ba su hada layukan su da NIN ba.
Yayin da mutane ke cikin halin kunci a Najeriya, wasu jarumai da mawaka sun fara shan suka musamman kan zaben Tinubu a lokacin kamfen zaben 2023.
Yayin da ake ci gaba da shari'ar matashiyar 'yar Tiktok a jihar Kano, Murja Ibrahim Kunya, Kotun Shari'ar Musulunci ta sake hukunci kan zarginta da ake yi.
Shafukan ra'ayi da sada zumunta
Samu kari