Ibadan
Gwamnatin jihar Oyo ta tabbatar da fara aikin rusau a wasu kauyuka da ke kusa da titin Circular, wani shugaban yanki ya yi ikirarin an rushe gidaje kusan 500.
Gwamnatin jihar Oyo karkashin Gwamna Seyi Makinde ta dakatar da basaraken Ilua daga kan mulki saboda barkewar rikici a kauyuka 2 kuma ana zargin da sa hannunsa.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya saka ma’aikata hawaye a jihar yayin da ya amince da tsawaita biyan kudaden rage radadin cire tallafi har na watanni shida.
Gwamnatin jihar Oyo ta rufe wani babban coci a birnin Ibadan da ke jihar saboda yawan damun jama'ar yankin da kararraki wanda ya hana su sakat a gidajensu.
Majalisar jihar Oyo ta bukaci cafke shugaban Fulani, Seriki Chumo kan zargin kisan manomi da jami'in tsaron Amotekun a yankin Iwajowa da ke jihar.
An tattabatar da tashin gobara a ofishin hukumar zabe da ke karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas, jihar Oyo a safiyar ranar Juma’a, 26 ga watan Janairu.
Wani jirgin sama dauke da manyan mutane guda 10 a cikinsa ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Samuel Ladoke Akintola da ke birnin Ibadan a jihar Oyo.
Gwamnatin jihar Oyo karkashin Gwamna Seyi Makinde ta tabbatar da cewa an gano ƙarin gawarwakin mutane 2 a wurin da wani abu ya fashe a Ibadan ranar Talata.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde,ya nemi amincewar majalisar dokokin jihar domin ciyo bashin Naira biliyan 150 daga cibiyoyin hada-hadar kudi na Afrexim da Access.
Ibadan
Samu kari