Yan Kwallo
An dakatar da 'dan wasan Juventus, Paul Pogba daga buga kwallon ƙafa na tsawon shekara hudu bisa samunsa da laifin amfani da sinadarai masu kara kuzari.
Hukumar kwallon kafa ta kasar Saudiyya ta dakatar da dan wasan kungiyar Al Nassr, Cristiano Ronaldo kan nuna rashin da'a yayin wasa a karshn mako.
Tsohon mai tsaron gida na tawagar Super Eagles ta Najeriya, Vincent Enyeama, ya rasa mahaifinsa. Enyeama yanzu ya zama maraya bayan rasuwar mahaifiyarsa a baya.
A tsawon lokaci, an samu wasu 'yan wasan kwallon kafa da aikata laifuka daban-daban a wajen wajen filin wasa kuma an yanke musu hukunci bisa doka.
Wata kotu da ke zamanta a kasar Andalus ta yanke wa tsohon dan wasan Barcelona, Dani Alves hukuncin daurin shekaru hudu da watanni 6 a gidan gyaran hali.
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa da mai tsaron baya, Shehu Abdullahi, sun ziyarci mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero bayan gama gasar AFCON 2023.
An shiga jimami yayin da tsohon dan wasan kasar Jamus da Bayern Munich, Andreas Brehme ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 63 a kasar Jamus.
An zargi golar Ivory Coast da sanya guraye a wasan karshe da suka buga da Najeriya a kwanakin baya da suka gabata. An bayyana gaskiyar abin da kr faruwa.
An yi ta yada wani faifan bidiyo mai nuna cewa mai tsaron gidan Ivory Coast ya yi amfani da laya a wasan karshe na AFCON 2023 tsakaninsu da Najeriya.
Yan Kwallo
Samu kari