Nade-naden gwamnati
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya damu matuka da tsadar kayan abinci kuma ya kuduri aniyar samar da abinci a farashi mai sauki, in ji ministan yada labaran sa.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, sauyin yanayi na yin tasiri ga rayuwa da lafiyar bil'adama, da wannan gwamnatin Nijeriya ta kuduri aniyar dasa itatuwa miliyan 6.
Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da jawo matasa yana ba su muƙamai a gwamnatin tarayya, a wannan karon ɗan shekara 36 ya zama shugaban hukumar CREDICORP.
Kotun CCB ta dakatar da Rimingado ne biyo bayan zarginsa da ake yi da aikata laifuffuka da suka shafi karbar cin hanci da karya dokar aikin gwamnati.
Gwamnatin tarayya ta nada jarumar fina-finai Rahama Sadau mamba a kwamitin gwamnati da ke kula da shirin saka hannun jari a fannin kirkire-kirkiren zamani (iDICE).
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi sababbin nade-nade guda biyar a gwamnatinsa. Daga ciki akwai na shugaban hukumar kula da harkokin majalisar dokokin jihar.
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naɗin ɗan Kwankwaso da kuma wasu mutum 3 a matsayin sababbin kwamishinonin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa.
Sanata Plang ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa majalisar dattawa na shirin tunɓuke Sanata Godswill Akpabio, ya ce babu wani abu mai kama da haka.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya ce naɗin da kwmaishina ya yi na hadimai 273 naɗi ne ka girmamawa amma gwamnati ba za ta rika biyansu albashi ba.
Nade-naden gwamnati
Samu kari