Aikin noma
Jama’an gari sun sace abinci da aka tarwatsa wurin ajiyan kaya a birnin Abuja. Bisa dukkan alamu jami’an tsaro ba su ankara da wuri ba ko kuwa ba a iya kai dauki ba.
Yayin da ake shan fama da tsadar abinci a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan lokacin da za ta fara rabon kayan hatsi na tan dubu 42 a jihar Neja
Mun kawo labarin inda aka kwana game da alkawarin raba kayan abinci saboda ana yunwa. An tanadi metric 42, 000 a cikin 102, 000, za a fara rabawa talakawa.
Ministan tattalin arzikin kasa, Olawale Edun ya ce farashin abinci zai fado. Gwamnatin tarayya za ta raba buhuna 1, 407,205 domin farashin abinci ya sauko.
A lokacin da ake neman abinci a Najeriya, sai ga motoci za su tsallaka Nijar. Mai magana da yawun bakin hukumar ZARTO a Zamfara ya tabbatar da wannan zance.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi jan-kunne a game da hadarin bude iyakoki a shigo da abinci. Tinubu ya ki daukar shawarar Kashim Shettima a kan kayyade farashin abinci
Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin kafa hukumar kayayyakin masarufi da za ta daidaita tashin farashin kayayyakin abinci a kasar da kuma bunkasa harkar noma.
Watsar da tsarin tallafin fetur ya jawo yunwa da wahalar rayuwa. Ministocin kasafi da na aikin gona su ka yi wa Sanatoci bayanin nan a majalisar dattawa.
Gwamnaton tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta shirya karya farashin kayan abinci a kasar nan don talaka ya huta.
Aikin noma
Samu kari