Yan bindiga
'Yan majalisa takwas da majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da su sun ce 'yan daba na farautar rayuwarsu saboda sun fallasa ta'azzarar tsaro a jihar.
Jami'an tsaro na 'yan sa kai, sun samu nasarar tura kasurgumin shugaban 'yan bindigan, da ya dade yana addabar mutane a jihar Katsina zuwa lahira.
An bayyana yadda tsagerun 'yan bindiga suka sako dalibai mata da suka sace a jihar Zamfara. An ruwaito cewa, sun sako su ne bayan shafe wata tara a tsare.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a jihar Anambra. A yayin harin dai sun kona wani dan banga har lahira bayan sun farmaki ofishinsu.
Wasu sojojin Najeriya sun rasa rayukansu a jihar Delta bayan an yi musu wani mummunan kwanton bauna. Hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta tabbatar da faruwar lamarin.
Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun tashi haikan domin kawo karshen matsalar rashin tsaron da yankin ke fama da ita, inda suka kafa sabuwar rundunar tsaro.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar PDP a jihar Edo. 'Yan bindigan sun sace shugaban jam'iyyar ne bayan ya gama ganawa da gwamna.
An shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya dauki hanyar tattaunawa da 'yan bindiga don ceto dalibai da matan da aka sace a jihohin Kaduna da Borno.
Wasu gungun miyagun 'yan ta'adda dauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a wani kauye da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, a ranar Asabar.
Yan bindiga
Samu kari