Jihar Ekiti
Oba Adebayo Fatoba, babban basarake a jihar Ekiti, ya bayyana yadda ya tsira daga hannun masu garkuwa da mutanen da suka halaka takwarorinsa biyu.
An bayyana yadda aka ga wasu daliban da aka sace sun samu 'yanci bayan shafe kwanaki kadan a hannun 'yan bindiga a wani yankin jihar Ekiti da ke Kudu maso Yamma.
Iyayen yaran makaranta da 'yan bindiga suka sace a jihar Ekiti sun koka kan halin da suke ciki. Sun ce maharan sun bar yaran da yunwa sannan ga duka.
'Yan bindigar da suka yi awon gaba da daliban makaranta a jihar Ekiti sun rage kudin fansarsu zuwa naira miliyan 15.Sun yi barazanar kashe su idan ba a biya ba.
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun damƙe mutane 13 da ake zargi suna da hannu a kisan da aka yi wa sarakuna 2 ranar Litinin a jihar Ekiti.
Ministan harkokin ci gaban ma'adanai, Dele Alake ya nesanta kansa da dukkan fastocin yakin neman zaben da ke yawo a soshiyal midiya cewa zai nemi takara a Ekiti.
A ranar Talata, 30 ga watan Janairu, Sanata Shehu Sani ya ce ya zama dole a hukunta wadanda suka kashe sarakunan Ekiti biyu. Ya yi addu’ar Allah ya ji kansu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhihinsa kan kisan da aka yi wa wasu sarakunan gargajiya a Ekiti, ya kuma umarci ceto daliban da aka sace a jihar.
Wani dan majalisar wakilai ya kasa danne zuciyarsa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar Ekiti. Dan majalisar ya fashe da kuka yayin da ya nemi a kai dauki.
Jihar Ekiti
Samu kari