Ado Doguwa
Kungiyar C3GR ta bukaci Shugaba Tinubu da kakakin majalisa, Abbas Tajudden da kada su ba wa Abdullahi Ganduje da Ado Doguwa mukamai saboda zargin da ke kansu.
Babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja ta ɗage sauraron ƙarar gwamnatin jihar Kano da Alhassan Ado Doguwa bisa zargin kisan kai da ake masa.
Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga sake cafke Doguwa bisa zargin kisan kai.
Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ya roki mambobin majalisar da ke takara kan su janyewa Tajuddeen Abbas takararsu domin a samu.
Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf(wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya sha alwashin sake bude shari’ar kisan kai da ake yi wa Alhassan Ado Doguwa.
Ma'aikatar shari'a ta jihar Kano ta ce binciken da ta gudanar kan tuhumar da ake yi wa Alhassan Doguwa kan laifin kisan, ya nuna cewa ba a same shi da laifi ba.
Ƴan sanda a jihar Kano, sun gabatar da rahoton bayanai kan zargin da ake yi wa Alhassan Ado Doguwa, na laifin kisan kai. An mika takardun ofishi Antoni Janar.
Takarar Majalisa ta canza domin Alhassan Ado Doguwa ya koma goyon bayan Tajuddeen Abbas. Doguwa ya fasa neman takara a majalisa tun da jam’iyya ta raba gardama.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Najeriya Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa zarge-zargen da ake mi shi na kisan kai ba za su hana shi riƙe muƙami ba
Ado Doguwa
Samu kari