Hawayen Murnar da Nayi a kan Buhari Ya Dawo na Takaici inji Tsohuwar Masoyiya
- Hajiya Yadoma Bukar Mandara ta dawo rakiyar Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari
- Bayan shekaru bakwai a kan karagar mulki, Yadoma Mandara ta fahimci an yaudare ta
- Mandara mai shekara 34 tayi magana a Twitter, tana cewa tana kukan bakin ciki a yau
Borno - Yadoma Bukar Mandara ta na cikin wadanda ba su jin dadin yadda abubuwa suke tafiya a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Da take magana a shafinta na Twitter a ranar Juma’a, 29 ga watan Yuli 2022, Yadoma Bukar Mandara ta tabbatar da irin bakin cikinta.
Wannan Baiwar Allah take cewa hawayen da ta zubar saboda farin cikin nasarar Muhammadu Buhari, ya zama na bakin-ciki yau.
A cewar Yadoma Mandara, Muhammadu Buhari ya yi wasa da hankalin mutanen kasar nan.
“Ya Mai girma Muhammadu Buhari, hawayen farin cikin da na zubar a lokacin da ka lashe zabe, sun zama na bakin ciki da takaici a yau.
Lallai kayi wasa da hankalin mu.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babu wanda zai gyara Najeriya
An ji tana cewa tun da har Buhari wanda ake ganin zai gyara Najeriya ya gaza, ta cire rai da cewa akwai wani mahalukin da zai ceci jama’a.
“Tun da Mai ceton ‘Yan Najeriya – Buhari ya gaza, duk da yadda na sa rai a kan shi. Na hakura da cewa wani zai gyara kasar nan.
“Mu na zaune kurum a hannun Allah. Ni ce shugabar kasar kai na, na hakura da neman wani.
- Yadoma Bukar Mandara
Wacece Yadoma Mandara?
Yadoma Mandara ita ce ‘Yar auta a gidan Zannah Bukar Umaru Mandara, wani ‘dan siyasa wanda ya yi suna musamman a Borno
A 2013 ne Zanna Dujiman kasar Borno watau Alhaji Bukar Umaru Mandara ya bar Duniya, yana mai shekaru fiye da 80 da haihuwa.
Legit.ng Hausa za ta iya tuna cewa Yadoma Mandara ta shigo gari ne a lokacin da ta halarci taron CONFAB da aka yi a shekarar 2014.
An haifi Yadoma ne a Maris na shekarar 1990, don haka ta zama mafi karancin shekaru a cikin wadanda suka je taron kasar.
Tikitin Musulmi-Musulmi
Ku na da labari wasu kiristocin Arewa sun yi fushi a dalilin ba Kashim Shettima tikiti. Irinsu Solomon Dalung da sun bar APC sun soki lamarin.
Babachir David Lawal yace za su yaki Jam’iyyar APC da addu’o’i da katin zabe a 2023. Shi kuma Yakubu Dogara yana ganin APC tayi babban kuskure.
Asali: Legit.ng