2023: Mace Ta Maye Gurbin Dan Takarar Shugaban Kasa A Wata Jam'iyyar Najeriya
- Alhaji Yusuf Mamman Dantalle, Shugaban Jam'iyyar Allied People’s Movement kuma shugaban jam'iyyar ya janye daga takarar shugaban kasa na 2023
- Princess Chichi Ojei, fitacciyar yar siyasa haifaffiyar Jihar Delta kuma yar kishin kasa ce ta maye gurbinsa a matsayin yar takarar shugaban kasa
- Mamman Dantalle ya ce shi da sauran shugabannin jam'iyyar suka yanke shawarar don sunyi imanin Najeriya na bukatar kwarewa, basira da jajircewar mace
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Shugaban Jam'iyyar Allied People’s Movement (APM) kuma dan takarar shugaban kasarta a zaben 2023, Alhaji Yusuf Mamman Dantalle ya janye daga takarar shugaban kasar, rahoton Leadership.
A cikin sanarwar da ya rattabawa hannu da kansa ya kuma raba wa manema labarai a Abuja, Dantalle, ya ce shugabannin jam'iyyar sun hada kai sun zabi Princess Chichi Ojei, fitacciyar yar siyasa haifafafiyar Jihar Delta, yar kishin kasa kuma shugaba ta maye gurbinsa.
Najeriya na bukatar jajircewa da kwarewar mace a 2023, Dantalle
Ya ce janyewarsa alheri ne ga jam'iyyar, ya kara da cewa hakan zai karfafawa APM gwiwa wurin cin zaben shekarar 2023. Ya jaddada cewa APM ce kadai jam'iyyar da ta tsayar da mace matsayin yan takarar shugaban kasa, yana cewa kasar a yau tana bukatar kwarewa, basira, da jajircewa na mace.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bada tabbacin cewa sabuwar yan takarar shugaban kasa na APM din ta cancanta kuma tana da goyon bayan miliyoyin magoya baya da yan jam'iyya.
Ya yi alkawarin cewa jam'iyyar za ta kafa tawagar yakin neman zabe wanda za ta tsara yadda za a karfafa wa Najeriya gwiwa su yi rajista kuma su karbi katin zabe su jefa kuri'a su zabi APM, domin kuri'unsu za su yi tasiri.
Yayin da ya ce aikin da ke gabansu babba ne kuma yana bukatar kwarewar da jajircewar shugaban jam'iyya, ya yi alkawarin tare da sauran shugabannin APM za su taimakawa jam'iyyar ta yi nasara a zaben 2023.
Ya ce don hakan ne ya janye takararsa na shugabancin kasa ya kuma bukaci yan Najeriya su yi zabe na basira su kuma zabi jam'iyyar ta APM a dukkan zabuka. Ya ce tare za mu gina kasa ta gari.
Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP
A wani rahoton, Rufai Ahmed Alkali, shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, na kasa ya ce kalaman da aka danganta da dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, ba a fahimce su ba, The Cable ta rahoto.
A ranar Asabar, Kwankwaso ya ce yana bawa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party, 'muhimmiyar dama' na zama mataimakinsa.
Asali: Legit.ng