An kuma: ‘Dan takaran APC a Kaduna ya tsaida mace ta zama Mataimakiyar Gwamna

An kuma: ‘Dan takaran APC a Kaduna ya tsaida mace ta zama Mataimakiyar Gwamna

  • Uba Sani wanda zai yi wa APC takarar Gwamna a jihar Kaduna ya zabi Hadiza Sabuwa Balarabe
  • Idan APC ta lashe zabe, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe za ta zarce a kan kujerar da ta ke kai tun 2019
  • Sanata Uba Sani ya bayyana haka a Twitter, ya ce Hadiza Balarabe ta dace da abokiyar takararsa

Kaduna - Bayan an dade ana sauraro, ‘Dan takaran APC a zaben sabon gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana wanda za ta zama abokiyar takararsa.

Sanata Uba Sani ya ayyana Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin wanda za ta zama ‘yar takarar mataimakiyar gwamnan Kaduna a APC a zaben 2023 mai zuwa.

Uba Sani ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 4 ga watan Yuli 2022, inda ya yi bayanin abin da ya sa ya dauki Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labor Party ta lallaba wajen mutanen Zakzaky, ta na nemawa Peter Obi kuri’u

A cewar ‘dan takarar, Dr. Hadiza Balarabe wanda ita ce Mataimakiyar gwamna tun 2019, ta taka rawar gani wajen nasarorin da Malam Nasir El-Rufai ya samu.

Jawabin Uba Sani

"Bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, ina farin cikin sanar da cewa na dauki Mai girma Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata a zaben gwamnan jihar Kaduna na 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Hadiza Balarabe ta bada gudumuwa sosai wajen nasarorin da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta samu wajen raya kasa da cigaban al’umma.
Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe
Mataimakiyar Gwamnar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe Hoto: fpvoices.org
Asali: UGC
Dr. Balarabe ta nuna dagewa, jajircewa, da iya aiki da jama’a a matsayin mataimakiyar gwamna, wannan ya sa mata kaunar masu ruwa da tsaki a jihar.

Kira ga jama'a su zabi APC

Saboda haka ina kira ga mutanen jihar Kaduna da su goyi bayan Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata, ina kuma kira su zabi APC.

Kara karanta wannan

Kungiyar da ta sayawa Tinubu Fom din N100m, ta ce Elrufai take goyon bayan ya zama mataimaki

Kuri’unku za su taimaka mana wajen kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba a jihar Kaduna. Tare za mu sa Kaduna ta zama abin yin misali."

- Uba Sani

Mai girma gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na Facebook. El-Rufai ne ya marawa Sani baya a zaben fitar da gwani.

Hadiza Sabuwa Balarabe

A zaben 2019 ne Hadiza Sabuwa Balarabe ta canji Marigayi Barnabas Bala Bantex a kujerar mataimakiyar gwamna, abin da ba a taba yi ba a tarihin jihar.

'Dan takaran APC watau Uba Sani ya fito ne daga Kaduna ta tsakiya (inda yake wakilta a majalisa), ita Balarabe mutumiyar Sanga ce a kudancin jihar.

Kafin nan ta rike hukumar kiwon lafiya ta jihar, Kaduna State Primary Health Care Agency.

Orubebe ya shiga APC

A Neja-Delta, ana da labari Jam’iyyar APC ta yi babban kamu a yankin da Goodluck Jonathan ya fito domin Elder Godsday Peter Orubebe ya yi rajista da APC

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan majalisa mai ci a wata jiha rigamu gidan gaskiya

Shugaban APC na karamar hukumar Burutu ya yi farin ciki da jin Elder Orubebe ya sauya-sheka, yanzu sun samu ‘Dan siyasan da ake ji da shi daga kasar Ijaw.

Asali: Legit.ng

Online view pixel