Faston da ya saba hasashen zabe ya ambaci ‘Dan takara 1 da ba zai kai labari a 2023 ba

Faston da ya saba hasashen zabe ya ambaci ‘Dan takara 1 da ba zai kai labari a 2023 ba

  • Shugaban cocin Adoration Ministry a Enugu ya yi hasashen Jam’iyyar LP ba za ta ci zaben 2023 ba
  • Rabaren Ejike Mbaka ya yi huduba a cocinsa, ya yi kaca-kaca da Peter Obi wanda ya ce marowaci ne
  • Fr. Ejike Mbaka ya zargi ‘dan takaran shugaban kasar da cin amanar Ojukwu saboda ya bar APGA

Enugu - Rabararen Ejike Mbaka wanda shi ne babban Limamin cocin Adoration Ministry da ke garin Eungu ya yi wani hasashe a game da zabe mai zuwa.

Rabararen Ejike Mbaka ya nuna cewa Peter Obi ba zai samu nasara a zaben 2023 ba. Rahoton nan ya fito daga gidan yada labarai na BBC Igbo a ranar Laraba.

Babban Faston ya ke cewa ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar LP matsolon mutum ne mai mako.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunnowa APC, ‘Yan adawa na iya karbe Jihar Shugaban kasa a zaben 2023

Dubban mutane sun halarci zaman cocin da Rabarren Mbaka ya yi wannan huduba a garin Enugu inda ya ce al’umma ba za su aminta da maras sakin hannu ba.

Atiku ya huta yanzu- Mbaka

A cewar malamin addinin, ‘dan takaran jam’iyyar PDP watau Abubakar Atiku ya nuna da gaske yake neman kujerar shugaban kasa domin ya raba jiha da Obi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

BBC ta rahoto Mbaka yana cewa tsohon gwamnan yana da ‘dan gashi don haka ba zai cin ma burinsa ba, muddin bai nemi Ubangiji afuwar laifin da ya yi ba.

Mbaka da Peter Obi
Fr. Ejike Mbaka da Peter Obi Hoto: Peter Obi, Adoration Ministry Enugu Nigeria - AMEN
Asali: Facebook

Mbaka ya zargi ‘dan siyasar da zagin Ubangiji bayan coci ya taimaka masa wajen zama Gwamna. Obi ya yi shekaru kusan takwas ya na mulki a jam'iyyar APGA.

Fittaccen Faston yake cewa ‘dan takaran na zaben 2023 ya ci amanar Marigayi Odumegwu Emeka Ojukwu saboda ya bar jam’iyyar APGA zuwa PDP da LP.

Kara karanta wannan

Bayan an kammala zaben APC, Fadar Shugaban kasa ta yi maganar ‘Dan takarar Buhari'

Jawabin Fasto Mbaka a coci

“An yi wa Peter Obi baki, ba zai kai labari ba (a zaben 2023), har sai ya zo ya tsuguna a mimbarin cocin Adoration.”
“Mutumin da bai kashe kudinsa ya ci abinci, shi ku ke son ku marawa baya? Ku na so mutane su zauna da yunwa ne?”
“Idan ya zama shugaban kasa, zai rufe cocinmu. Idan Ibo na neman wakilci a Najeriya, to ba irinsu Obi ake nema ba.”
“Shin ya kamata duk mutumin da ya ki taimakawa coci da sadaka ya zama shugaban kasa?”

- Ejike Mbaka

APC za ta dauki mataimaki

Rahotanni na nuna a yau mutanen Najeriya za su san abokin takarar Bola Tinubu a Jam’iyyar APC, da alamar takarar Musulmi-Musulmi na neman tabbata.

Asiwaju Bola Tinubu ya nuna sha’awar tafiya da yankin Arewa maso gabas, domin ana kishin-kishin din zai dauki Sanata mai-ci ya zama masa mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Arewa, da jerin kalubale 7 da suke jiran Peter Obi idan ya tsaya takarar Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel