An nemi Gwamna, Mataimakinsa da Sarki an rasa da Osinbajo ya je neman kuri’un APC

An nemi Gwamna, Mataimakinsa da Sarki an rasa da Osinbajo ya je neman kuri’un APC

  • Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara zuwa Jigawa inda ya zauna da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a Dutse
  • Osinbajo bai samu damar haduwa da Gwamna Badaru Abubakar da Mataimakinsa a garin Dutse ba
  • Mataimakin Shugaban kasar bai samu damar kai wa Sarkin Dutse gaisuwa ba, an ce ya yi tafiya

Jigawa - Mai girma Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kai ziyara zuwa jihar Jigawa domin samun goyon bayan ‘ya ‘yan APC a zaben tsaida gwani.

Premium Times ta ce Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da masu fito da ‘dan takara a jam’iyyar APC daga Jigawa ne a kokarinsa na zama ‘dan takarar shugaban kasa.

Labarin da mu ka samu shi ne Mai girma gwamna Muhammad Badaru Abubakar bai wajen taron yayin da Yemi Osinbajo ya zauna da ‘yan jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

'Dan takarar PDP ya fadi abin da ya sa Buhari ya gagara gyara Najeriya yadda ake sa rai

Haka zalika mun fahimci mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi bai samu halartar wannan zaman da aka yi a wani babban otel da ke garin Dutse ba.

Ina Gwamna da mataimakinsa?

Wani hadimin mataimakin gwamna, Ahmed Haruna ya shaidawa manema labarai cewa mai gidansa yana Abuja inda ake tantance shi a matsayin ‘dan takara.

Shi kuma Habibu Kila mai magana da yawun Badaru Abubakar, ya gagara yin bayanin abin da ya hana Mai girma gwamna tarbar tawagar Osinbajo a shekaran jiya.

Ana tunanin Gwamna Badaru wanda shi ma yana neman tikitin APC ya je Kano ne a lokacin.

Osinbajo ya je neman kuri’un APC
Farfesa Yemi Osinbajo da 'Yan APC a Jigawa Hoto: @laoluakandeofficial
Asali: Facebook

Osinbajo bai ga Sarki ba

An tsara ziyarar ne ta yadda da farko Farfesa Osinbajo da mutanensa za su kai ziyarar ban-girma zuwa ga Sarkin Dutse, Mai martaba Nuhu Muhammad-Sunusi.

Kara karanta wannan

Tambuwal da 'Yan siyasa 3 da za su shiga zaben 2023 da niyyar takarar kujeru 2 a lokaci 1

A wani rahoton da ya fito daga jaridar a ranar Lahadi, an ji cewa mataimakin shugaban Najeriyan bai hadu da Alhaji Nuhu Muhammad-Sunusi kamar yadda ya so ba.

Mai martaba ya je Abuja

Sakataren masarautar Dutse, Wada Alhaji ya musanya jita-jitar da ake ji na cewa Mai martaba ya bar jihar Jigawa ne da ya ji labarin zuwa tawagar Yemi Osinbajo.

Wada Alhaji ya ce tun kafin Farfesa Osinbajo ya zo, an sanar da hadiminsa, Abdulraman Yola cewa Mai martaba ya na halartar wani taro da ake yi a garin Abuja.

An sanar da mai ba mataimakin shugaban kasar shawara cewa Galadiman Dutse Basiru watau Sanusi ne zai wakilci Mai martaba idan Osinbajo ya ziyarci fadar.

Kwanakin baya aka ji Sarkin Dutse, Muhammad-Sunusi yana yabon Rotimi Amaechi. Ministan sufuri yana cikin sauran masu neman kujerar shugaban kasa a APC.

Za a zabi Tinubu a Kaduna?

Kwanaki kun samu rahoto cewa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya karbi Bola Tinubu da ‘yan tawagarsa hannu biyu da aka yi zama da 'yan APC.

Kara karanta wannan

Osinbajo ya na sa ran doke Tinubu, Amaechi da kowa a APC, ya zama ‘dan takara a 2023

Gwamna Nasir El-Rufai ya tabbatarwa Duniya cewa ‘ya ‘yan APC na Kaduna duk su na tare da takarar Bola Tinubu wanda yake sa ran samun tikiti a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel