Masu cin gajiyar N-Power sun yi karo-karo, sun tara Miliyoyin Naira zasu siya wa ɗan takara Fom a Kano
- Ma'aikatan tsarin N-Power a jihar Kano sun taimaka wa Sha'aban Sharaɗa da kuɗi miliyan N10m don cimma burinsa a 2023
- Sharaɗa, ɗan majalisa mai wakilatar mazaɓar Kano Municipal, ya na daga cikin yan takarar gwamnan Kano karkashin APC
- Wata ƙungiya FJK ta bi sahun masu cin gajiyar shirin, ta tara wa ɗan majalisar wasu miliyan N10m na daban
Kano - Aƙalla yan Najeriya 2,700 dake cin gajiyar tsarin N-Power a jihar Ƙano ne suka yi karo-karon tara kudi miliyan N10m domin goyon bayan takarar gwamnan Sha'aban Sharaɗa, mamba a majalisar wakilan tarayya.
Wannan na zuwa ne bayan wata ƙungiyar ma'aikata duk a jihar Kano wacce ake wa laƙabi da Fitilar Jama’ar Kano (FJK) ta tattara Miliyan N10m domin taimaka wa cikar burinsa na zama gwamna.
Honorabul Sha'aban Sharada, a yanzu haka shi ne ɗan majalisa mai wakiltar Kano Municipal a majalisar wakilan tarayyan Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Haka nan kuma Sharaɗa ya na daga yan takarar dake hangen kujerar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen 2023 dake tafe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ya ma'aikata suka iya haɗa makudan kudi haka?
Da yake miƙa wa ɗan majalisan cakin kudin a madadin sauran ma'aikatan N-Power, shugaban su na jihar Kano, Abba Lawan, ya faɗi yadda suka yi namijin kokari suka haɗa kudin.
A jawabinsa ya ce:
"Kowane ma'aikaci ɗaya daga cikin mu ya ba da gudummuwar Naira Dubu N5,000 ta hanyar aje Dubu Ɗaya a kowane wata na tsawon watanni biyar."
A bangaren sa, yayin da yake karɓan gudummuwar a madadin ɗan majalisan, ɗaya daga cikin shugabannin FJK, Mansur Kurugu, ya ce kungiyarsu ba'a barta a baya ba, ta haɗa miliyan N10m don tallafawa ɗan majalisan.
Ana Shirin Sallah: Yan bindiga sun kashe Kwamandan jami'an tsaro, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara
A wani labarin kuma Fitattun Attajirai biyu sun lale miliyan N200m zasu siyawa mutum biyu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC
Wasu yan kasuwa guda biyu yan asalin jihar Abia sun shirya lale makudan kuɗi Miliyan N200m don siya wa mutum biyu Fom a APC.
A wata sanarwa da suka fitar a Abuja , fitattun Attajiran sun ce sun gano kwarewa da salon mulki a jikin Sanata Ahmad Lawan da Orji Kalu.
Asali: Legit.ng