Tuna-baya: Yadda EFCC ta binciki sabon shugaban jam’iyar APC a kan satar Biliyoyi a 2010

Tuna-baya: Yadda EFCC ta binciki sabon shugaban jam’iyar APC a kan satar Biliyoyi a 2010

  • A watan Maris na 2010 ne Economic and Financial Crimes Commission ta kama Abdulahi Adamu
  • Femi Babafemi ya ce hukumar ta na zargin Adamu da badakalar kwangiloli a lokacin yana gwamna
  • Adamu ya yi gwamna na shekaru takwas a Nasarawa inda ake zargin an yi cuwa-cuwar kwangiloli
  • Wani rahoton ya na nuna cewa akwai alamar tambaya a game da karatun Sanatan na Nasarawa

Lafia – The Cable ta dauko wani rahoto da ya nuna a Maris shekarar 2010, hukumar EFCC ta shiga kotu da Abdullahi Adamu bisa zargin satar dukiyar al'umma.

Lauyoyin hukumar EFCC sun zargi Adamu da aikata laifuffuka 149 a lokacin yana rike da kujerar gwamna a jihar Nasarawa tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Adamu da wasu mutane 18 ne EFCC ta tuhuma da laifin sace Naira biliyan 15 daga asusun jiha.

Kara karanta wannan

Ai ga irinta nan: Kalaman ‘Dan takarar Shugaban APC sun yi masa illa, an juya masa baya

Sauran wadanda aka shiga kotu da su sun hada da tsofaffin jami’an gwamnatin jihar Nasarawa da wasu ‘yan kwangila da suka yi aiki a lokacin mulkin Adamu.

Rahoton ya ce an kai wannan kara ne gaban Alkali mai shari’a David Okorowa a babban kotun tarayya da ke zama a garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Lauya ya kare Adamu a gaban kotu

Lauyan da ya tsayawa tsohon gwamnan na Nasarawa a lokacin ya shaidawa kotu cewa wanda ake tuhuma bai aikata laifin da gwamnati ta ke jifansa da shi ba.

Sannan lauyan ya kafa hujja da cewa laifuffukan da EFCC ta ke binciken sun faru ne a jiha, don haka jami’an hukumar ba su da hurumin da za su yi bincike a kai.

Sabon shugaban jam’iyar APC
Abdullahi Adamu ya na rantsuwar APC Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Hannun kwamishinan kananan hukumomi

An zargi Adamu da kwamishinan kananan hukumominsa Halilu Bala Usman da cire N2,456,000,000 na tsawon wata 63 daga asusun kananan hukumomi.

Hakan ta sa Okorowa ya hakikance a kan cewa Sanata Adamu yana da bayanin da zai amsa a kotu.

Adamu ya daukaka kara zuwa gaba

A 2013, sai aka ji Sanatan na yankin Nasarawa ta kudu ya shigar da kara a babban kotun daukaka kara, yana mai kalubalantar matsayin da kotun tarayyar ta dauka.

Rotimi Oguese shi ne wanda ya tsayawa Adamu a kotun daukaka kara. Rahotanni sun bayyana mana cewa tun lokacin ba a sake jin komai a wannan shari’ar ba.

A shekarar 2016 sai aka ji ‘dan siyasar yana cewa an yi fatali da karar. Zuwa wannan lokaci, Adamu ya sauya-sheka daga PDP, ya shiga jam’iyyar APC mai mulki.

Wasu zargin na dabam a wuyansa

A wani kauli na SaharaReporters, duk da Adamu ya karanta ilmin shari'a a jami'ar Jos, ana zargin bai taba zuwa makarantar koyon aikin shari'a na lauyoyin kasa ba.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Sannan a shekarar 2017 EFCC ta ce za ta kai Nuraini Adamu kara a kotu a kan zargin satar wasu Naira miliyan 92, amma har yau shiru. Nuraini ‘da ne ga Sanatan.

Akwai datti a jikin shugabannin APC?

Shekaru goma kenan da faruwar wannan abin, sai aka ga ana rantsar da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na kasa a taron Abuja.

A daidai wannan lokaci kuma aka ji cewa Sanata Iyiola Omisore ya zama sakataren APC. Shi ma EFCC ta taba shari'a da shi bayan zargin kisan kai da aka yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel