‘Ya ‘yan Jam’iyya su na neman yi wa Buhari kunnen-kashi, ba su tare da ‘Dan takararsa

‘Ya ‘yan Jam’iyya su na neman yi wa Buhari kunnen-kashi, ba su tare da ‘Dan takararsa

  • Wadanda aka yi tafiya tare da su a jam’iyyar CPC suna goyon bayan Tanko Al-Makura a zaben APC
  • Zabin wadannan tsagi ya ci karo da ra’ayin shugaban kasa – wanda yake tare da Abdullahi Adamu
  • Okoi Obono-Obla yana ganin Al-Makura wanda ya fito daga bangaren CPC ya dace ya rike jam'iyya

Abuja - Wasu daga cikin wadanda suka kasance masu ruwa da tsaki a tsohuwar jam’iyyar CPC, su na adawa ga Abdullahi Adamu a zaben shugaban APC.

Wani rahoto da ya fito daga Daily Trust ya ce wadanda suka rike shugabanci a majalisar NWC da sauran kwamitoci a CPC ba su goyon bayan Abdullahi Adamu.

Wadannan mutane su na ganin ya kamata a samu wanda ya fito daga bangaren CPC – Daya daga cikin jam’iyyun da suka narke a APC, ya zama shugabanta.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar Arewa yana tare da Buni, ya jero cigaban da ya kawo APC a shekaru 2

Jam’iyyu kusan hudu ne suka hadu aka kafa APC a 2013. Jam’iyyun hamayyar a lokacin su ne ACN, ANPP, CPC da wasu tsagin APGA da wasu ‘yan nPDP.

Sanata Abdullahi Adamu yana cikin ‘yan PDP da suka shigo jam’iyyar APC mai mulki. Su kuma wadannan gungu su na mara baya ne ga Tanko Al-Makura.

Matsayar su Okoi Obono-Obla

Sakataren wannan kungiya, Okoi Obono-Obla ya zanta da manema labarai a garin Abuja, inda ya yi tir da rikicin cikin gidan da yake damun jam’iyyar APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Al-Makura
Shugaban kasa tare da Umaru Tanko Al-Makura Hoto: @Mbuhari
Asali: Twitter

Okoi Obono-Obla yana ganin wadannan sabani da rabuwar kai sun yi wa APC illa a zabukan baya. Lauyan yana kuma zargin APC ta saki layin da aka kafa ta a kai.

Rahoton ya ce tsohon shugaban kwamitin na SPIP yana ganin tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-makura ne ya fi dacewa ya karbi jagorancin APC.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa a APC, an samu Sanatoci sun ce ba a tunbuke Mala Buni daga matsayinsa ba

Obono-Obla ya fadawa ‘yan jarida cewa wannan karo ya kamata tsagin CPC su fito da shugaba, a lokacin da ake ganin fadar shugaban kasa tana bayan Adamu.

Daga cikin abin da ya sa suke goyon bayansa shi ne kwararren ‘dan siyasa ne kuma wanda ya yi zarra a kasuwanci, sannan ya kware a wajen rikon jam’iyya.

Obono-Obla ya ce Al-Makura mutum ne mai kishin kasa, wanda zai iya tafiya da kowa a jam’iyya. A karshen watan nan ne dai za ayi zaben shugabannin na APC.

Buhari yana yin Abdullahi Adamu?

Kwanaki ne ku ka ji cewa rahotanni sun ce Muhammadu Buhari ya zabi Abdullahi Adamu a matsayin ‘dan takarar da yake so ya zama shugaban jam’iyya a APC.

Ana tunanin Muhammadu Buhari ya nuna yana tare da Sanata Adamu a zaben mai zuwa. Shi dai Sanatan na jihar Nasarawa ya musanya wannan magana da kansa.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 9 da za su iya asarar kujerunsu a kotu a sakamakon sauya-sheka zuwa APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel