‘Dan Majalisar Arewa yana tare da Buni, ya jero cigaban da ya kawo APC a shekaru 2

‘Dan Majalisar Arewa yana tare da Buni, ya jero cigaban da ya kawo APC a shekaru 2

  • Smart Adeyemi ya ce ‘yan majalisar dattawa ba su san an sauke Mai Mala Buni daga shugaban APC ba
  • ‘Dan majalisar mai wakiltar Kogi ta yamma ya ce an ga cigaba a karkashin jagorancin Mala Buni
  • Sanata Adeyemi yana ganin cewa Gwamna Buni ne ya mikawa Abubakar Sani Bello rikon jam'iyya

Abuja - A ranar Alhamis 10 ga watan Maris 2022, Sanatan Kogi, Smart Adeyemi ya bayyana cewa ba su da labarin abin da ya faru na canjin shugabanci a APC.

Channels TV ta rahoto Sanata Smart Adeyemi yana cewa shi da sauran abokan aikinsa a majalisar dattawa ba su san cewa an sauke Mai Mala Buni ba.

Da aka yi hira da shi a shirin siyasar nan na Politics Today a gidan talabijin, Adeyemi ya nuna cewa yana cikin magoya bayan Gwamna Buni a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Mai Mala bai bani wata wasika ba: Gwamna Neja ya yi martani mai zafi

‘Dan majalisar ya na da ra’ayin cewa Buni ne ya rubutawa Abubakar Sani Bello takarda, ya bukaci ya rike jam’iyya har zuwa lokacin da zai dawo daga kasar waje.

Wasikar Mala Buni

“Akwai takardar da Mai Mala Buni ya rubuta, yana cewa ya yi tafiya. A wannan takarda, ya mika jagoranci ga gwamnan jihar Neja.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A iyaka saninmu a majalisar dattawa, ba mu da labarin cewa shugaban kasa ya bada umarni a sauke shugaban rikon kwaryan APC.”

- Smart Adeyemi

‘Dan Majalisan Kogi
Sanata Smart Adeyemi a Majalisa Hoto: @sensmartadeyemi
Asali: Twitter

Buni ya kawowa APC cigaba

A cewar Smart Adeyemi, jam’iyyar APC mai mulki ta samu wasu nasarori a karkashin Mala Buni, bayan ya karbe ta a lokacin da ake tsakiyar fama da rigingimu.

“Siyasa ce kurum. Mai Mala Buni ya yi kokarin gaske, ya jawo kwararrun mutane, gwamnoni, tsofaffin sojoji, dattawa, ya shigo da su APC.”

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

“A dalilin haka, a yau APC ta kara karfi. Asali ma, akwai bukatar mu yi masa godiya ne.”
“Buni ya zo sa’ilin da ake rigima a APC, lokacin da ta ke neman wargajewa. Shi ya dinke barakar jam’iyya, yanzu ta na shirin kai ga yin nasara.”

- Smart Adeyemi

Ra'ayin Sanatocin jam'iyya

A tsakiyar makon nan ne aka ji Sanatocin APC sun yi zama na musamman a game da rikicin shugabanci, sun ce babu gaskiya a zancen tsige Mai Mala Buni.

Sanata Yahaya Abdullahi ne ya bayyana wannan, ya ce Abubakar Sani Bello shugaban riko kwarya ne, kuma zai sauka daga kujerar da zarar Buni ya dawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel