Zaben tsaida ‘dan takarar Gwamna ya jawo yamutsi, an tsaida ‘yan takara 2 a PDP

Zaben tsaida ‘dan takarar Gwamna ya jawo yamutsi, an tsaida ‘yan takara 2 a PDP

  • An shirya zabuka har biyu domin fitar da ‘dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben jihar Osun
  • Sanata Ademola Adeleke ne ya lashe zaben da Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa ya shirya a jiha
  • Shi ma Dotun Babayemi yana ikirarin shi ne ‘dan takarar PDP bayan ya yi nasara a wani zaben dabam

Osun - Sanata Ademola Adeleke da Dotun Babayemi duk su na ikirarin su ne ‘yan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben gwamnan jihar Osun.

Vanguard ta ce kowanensu ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da bangarensa suka shirya. An gudanar da zabukan ne a ranar 8 ga watan Maris 2022.

Bangaren PDP da Sunday Bisi yake jagoranta sun shirya zaben su a filin wasa da ke garin Osogbo, mutanen Wale Ojo sun yi nasu zaben a cibiyar WOCDIF.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 9 da za su iya asarar kujerunsu a kotu a sakamakon sauya-sheka zuwa APC

Sanata Lawrence Ewurujakpo ya sanar da sakamakon na su a zaben da cewa Sanata Adeleke ne ya yi nasara da kuri’a 1, 887, ya doke sauran ‘yan takaran.

A cewar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Fatai Akinbade, Akin Ogunbiyi da Babayemi ba su da ko kuri’a daya, sai Sanya Ominrin ya samu kuri’u hudu.

‘yan takara 2 a PDP
Yan takarar PDP a Osun Hoto: Dailypost/Sunnews
Asali: UGC

Wani zaben na dabam

A zaben da Dotun Babayemi ya samu nasara, Adelani Ajanaku ne ya bada sanarwar sakamakon zabe inda aka ji Babayemi ya samu nasara da kuri’u 1, 781.

A cewar Ajanaku, Omirin ya samu kuri’u 16, Ogunbiyi ya samu 23; Akinbade ya tashi da 28, Dele Adeleke ma ya samu kuri’u 32 a zaben tsaida ‘dan takarar.

Jawaban 'yan takara

Shi dai Dotun Babayemi ya bayyana cewa tun da ya samu tikitin jam’iyya, zai yi kokarin canza halin da al’umma suke ciki idan har ya zama gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Premium Times ta ce duka bangarorin sun samu sabani a kan wadanda za su kada kuri’a a zaben.

A gefe guda, Sanata Adeleke ya ce a matsayinsa na ‘dan takara, akwai bukatar ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP su hada-kai domin tika jam'iyyar APC da kasa a filin zabe.

Adeleke wanda ya taba neman takarar gwamna ya ce mutanen Osun sun tagayyara a hannun gwamnatin APC, don haka akwai bukatar PDP ta dare kan mulki.

'Yan siyasan da suke ruwa

A jiya kun ji akwai wasu ‘yan siyasa da-dama da suka canza sheka zuwa APC da za su iya rasa kujerunsu a kotu ganin hukuncin da aka yi ga gwamnan Ebonyi.

Hukuncin Inyang Ekwo zai iya shafan gwamnonin jihar Zamfara, Kuros Riba da suka koma APC. Sannan kuma akwai wasu Sanatoci biyar da suka yi watsi da PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel