Ganduje da jerin Gwamnoni da Ministoci 6 da suka ba yara da 'yanuwansu mukamai masu tsoka

Ganduje da jerin Gwamnoni da Ministoci 6 da suka ba yara da 'yanuwansu mukamai masu tsoka

  • Akwai wasu ‘yan siyasar Najeriya da suka jawo ‘ya ‘yansu da ‘yanuwansu a cikin gwamnatinsu
  • Daga cikin wadannan ‘yan siyasa akwai Gwamna Rotimi Akeredolu, Ifeanyi Okowa da Jonah Jang
  • A lokacin da Rochas Okorocha yake mulki, ya nada ‘yaruwarsa a matsayin Kwamishinar farin ciki a Imo

Legit.ng ta kawo jerin wasu daga cikin masu mulkin da suka taba ba ‘ya ‘yansu mukamai a gwamnati, ko na mai bada shawara, ko cikin wani kwamiti.

Sai dai wannan rubutu bai yi niyyar zargin wani gwamna ko minista ba, sai dai a kawo rahoto a yadda yake, domin nadin mukaman bas u saba wata doka ba.

1. Abdullahi Umar Ganduje

‘Diyar Gwamnan Kano, Amina Ganduje, tana cikin kwamitin yaki da COVID-19 da aka kafa a 2020. Dr. Ganduje kwararriya likita ce wanda tayi karatunta a Maiduguri, Zaria da kuma Kano.

Read also

Da dumi-dumi: Tsohon kwamishinan jihar Delta, Kenneth Okpara ya mutu

2. Jonah Jang

Sanata Jonah Jang ya dama da ‘dan cikinsa, Yakubu Jang da yake gwamna a jihar Filato. Yaronsa ya taba zama Kwamishinan filaye, bayan ya yi mai bada shawara a kan ayyuka na musamman.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jerin Gwamnoni
Rotimi Akeredolu, Ifeanyi Okowa da Jonah Jang
Source: UGC

3. Ifeanyi Okowa

A jerin na mu akwai gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, wanda ya nada ‘diyar cikinsa, Marilyn Okowa-Daramola a matsayin mai bada shawara a kann harkar karfafawa ‘yan mata.

4. Rochas Okorocha

Rochas Okorocha ya nada yayarsa, Ogechi Ololo a cikin kwamishinoninsa da yake gwamna a Imo. Sannan surukinsa, Uche Nwosu ya yi shugaban ma’aikatan fada kafin ya yi takarar gwamna.

5. Paul Tallen

A shekarar 2020, Ministar harkokin mata, Paul Tallen ta nada ‘yarta watau Violet Osunde, ta zama mai ba ta shawara. Osunde tayi karatunta a jami’o’I’in Plymouth da Brunel da ke Birtaniya.

Read also

Yadda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya canza gidan siyasa sau 6 a shekara 7

6. Rotimi Akeredolu

Kwanan nan Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya nada ‘dan shi Babajide Akeredolu a matsayin shugaban hukumar PPIMU mai sa ido a kan yadda ayyukan gwamnati suke tafiya.

Mista Babajide Akeredolu ya shiga cikin mukarraban gwamnan jihar Ondo. A baya an taba jin Rotimi Akeredolu SAN yana cewa zai iya ba 'dan na sa mukami, kuma dole a zauna lafiya.

Okorocha da Uche Nwosu

Gabanin zaben 2019, an ji cewa Gwamnan Jihar Imo watau Rochas Owele Okorocha yayi nasarar samun tikitin Sanata sannan ya kuma tsaida Surukin sa a matsayin ‘Dan takarar Gwamna.

Daga baya Jam’iyyar APC ta hana Uche Nwosu tikitin, dole ya yi takara a jam'iyyar adawa ta AA.

Source: Legit.ng

Online view pixel