FUTO: Shahararren Farfesa ya hada Dr. Pantami da Fani-Kayode, duk ya yi masu kaca-kaca

FUTO: Shahararren Farfesa ya hada Dr. Pantami da Fani-Kayode, duk ya yi masu kaca-kaca

  • Farfesa Farouk Kperogi da yake aiki a kasar Amurka ya yi wa Femi Fani-Kayode a wani rubutunsa
  • Farouk Kperogi ya yi raddi ga tsohon Ministan yayin da ya wanke Isa Pantami daga zargin zuku
  • Babban marubucin yana ganin Jami’ar FUTO ta saba doka da ta ba Dr. Pantami mukamin Farfesa

United States - Farfesa Farouk Kperogi yayi wani rubutu, inda wannan karo ya ragargaji Femi Fani-Kayode a kan yunkurin da yayi na kare Dr. Isa Ali Pantami.

A wani bayani da Femi Fani-Kayode ya yi, ya soki wadanda suka hurowa Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, wuta saboda kara masa matsayi zuwa Farfesa.

Farouk Kperogi, malami a wata jami’ar kasar Amurka, wanda ya dade yana sukar yadda aka yi wa Ministan karin matsayin da ya kira zuku, ya fito ya sake yin raddi.

Read also

Yadda Buhari ya tattaro biliyoyin da aka sace, aka boye a Amurka, Ingila da Switzerland

Farfesan yake cewa bai cika karanta rubuce-rubucen Femi Fani-Kayode ba, amma tun a 2006 ya gane cewa ‘dan kwaritsi ne, mai kwadayi, mai mugun ra’ayin addini.

A rubutun na sa, Kperogi ya dauko munanan kalaman da Fani-Kayode ya rika yi a game da jam’iyyar APC da ma yadda ya rika jifar Dr. Pantami da ta’addanci.

Bambancin addini ya sa aka hurowa Pantami wuta?

Masanin yace mutumin da ya taba zargin Ministan da hannu a kisan kiristoci a Najeriya, sai ga shi yau yana cewa ASUU ta taso shi a gaba saboda shi musulmi ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A game da zargin saboda addini aka matsawa Pantami lamba, Kperogi yace kusan duk wanda suka hurowa Pantami wuta a kan zukun da aka yi masa musulmai ne.

Yace masu sukar Pantami musulmai ne: Farfesa Abdulsamad Umar Jibia, Dr. Abdelghaffar Amoka, Dr. Nasir Mansir, Dr. Ali Abubakar Sadiq, da Dr. Abdulaziz Tijjani.

Read also

Kawai Don Yana Musulmi, FFK Ya Kare Sheikh Pantami Kan Matsayin Zama Farfesa

Dr. Pantami da Fani-Kayode
Isa Pantami, Fani-Kayode da Bello Matawalle Hoto: @RealFFK
Source: Facebook

Pantami bai dace ya zama Farfesa ba

“Fani-Kayode bai taba koyarwa a makaranta ba, bai san komai kan tsarin karin girma a jami’a ba, amma yana cewa Pantami ya cancanci zama Farfesa.”
“Ba don Fani-Kayode ‘ya zautu, kwakwalwarsa ta motsu ba, da ya san cewa Pantami bai dace ya zama Farfesa a Jami’ar FUTO ba. Sai mutum yana da digirin PhD, sannan ya koyar na shekara 12 sannan zai iya zama Farfesa a ka'idar jami’ar.”
“Pantami ya yi PhD ne a 2014, shekaru bakwai da suka wuce kenan, bai kai 12 ba. Gaba daya Pantami bai kai shekara goma yana koyarwa ba a rayuwarsa.” -Kperogi.

Farfesan bai tsaya nan ba, yace digirin PhD da Pantami ya yi, ba a fannin da ya zama Farfesa ba, ko da ana yin haka, shi bai yi wasu rubuce-rubuce a fannin ba.

Bugu da kari, Farfesa Kperogi yace a dokar Najeriya bai halatta Minista ya karbi aikin koyarwa ba, kamar yadda aka ba Pantami aiki a lokacin da ba zai shiga aji ba.

Read also

Bamu yarda da Farfesancin Isa Pantami ba, Uwar Kungiyar Malaman Jami'a ASUU

A karshe Kperogi yace Fani-Kayode ya kulla abokantaka da Pantami ne kurum saboda abin da zai samu. Har yanzu dai babu wanda ya maidawa malamin martani.

Femi Fani Kayode ya dawo APC

Kwanaki ne labarin sauya-shekar 'dan adawar ta zagaye ko ina. Sai dai Femi Fani-Kayode ya kare kan shi bayan komawarsa jam’iyyar APC da ya rika suka tun 2014.

Tsohon Minisan yace ya rika caccakar Muhammadu Buhari ne a da a bisa jahilci. Fani-Kayode yace ba don APC ta canza ba, da ba za a ji shi ya shiha jam’iyyar ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel