Murnar Jam'iyyar APC ta koma ciki, kotu ta karbe kujerar da ta lashe a zaben Jihar Legas

Murnar Jam'iyyar APC ta koma ciki, kotu ta karbe kujerar da ta lashe a zaben Jihar Legas

  • Kotun da ke karbar korafin zaben kananan hukumomi na Legas ta karbe kujerar Kansila a Oriade.
  • Alkalin kotun da ke sauraron kukan zaben kananan hukumomi, Morenike Obadina, ta yanke hukunci.
  • Morenike Obadina tace ‘dan takarar PDP, Mustapha Olanrewaju ne ya ainihin lashe zaben da aka yi.

Lagos - Babban kotun da ke sauraron korafin zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Legas, ya zartar da wani hukunci da ba a saba jin irinsa ba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa kotun daukaka karan da ke karbar korafe-korafe game da zabukan da aka shirya, ya ruguza nasarar jam’iyyar APC.

A ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, 2021, Alkali ya yanke cewa ‘dan takarar PDP, Mustapha Olanrewaju ne zababben kansilan mazabar Oriade ta I.

Read also

Zaben Anambra: Dalilai 5 da suka sa PDP ta sha mummunan kaye a zaben gwamna

Kotun karar zaben tace Mustapha Olanrewaju ne wanda ya lashe zaben kansila na Oriade A, a yankin Kirikiri, a karamar hukumar Oriade, a jihar Legas.

Alkali mai shari’a Morenike Obadina ta yanke wannan hukunci yayin da take jagorantar sauran Alkalai biyar a zaman da kotu tayi domin sauraron karar.

Zabe a Legas
Zaben kananan hukumomi a Legas Hoto: thesourceng.com
Source: UGC

An ba ‘dan takarar PDP takardar shaidar cin zabe

Rahoton yace kotun ta zauna ne a yankin Alausa, garin Ikeja, inda aka zartar da hukunci cewa hukumar LASIEC ta bada satifiket ga Mustapha Olanrewaju.

Kamar yadda kotu ta bada umarni, shugaban hukumar zabe na jihar Legas, Ayotunde Phillips ya mika satifiket din samun nasara ga ‘dan takarar jam’iyyar PDP.

Olusegun Ayedun ya wakilci shugaban LASIEC wajen gabatar da takardar shaidar samun nasarar, har ya yabawa Olanrewaju kan yadda ya nemi hakkinsa a kotu.

Read also

Zaben Anambra: Mata ta haihu jim kadan bayan kada kuri'a, ta rada masa suna Soludo

Da yake mika takardar shaidar lashe wannan zabe ga Olanrewaju a Yaba, Mista Olusegun Ayedun ya tabbatar da cewa hukumar LASIEC tana biyayya ga doka.

Shugaban sashen wayar da al’umma na LASIEC, Tope Ojo yace an karbe takardar nasarar da aka ba ‘dan takarar jam’iyyar APC, Onyeahasi, kuma ta tashi aiki.

Lucky Nosakhare Igbinedion ya ga ta kansa

A yau ne rahotanni suka ce lambar Lucky Nosakhare Igbinedion ya fito a ofishin EFCC inda ake zarginsa da wawurar wasu Naira biliyan 1.6 da yake gwamna.

Ana zargin tsohon gwamnan na jihar Edo da karkatar da wasu bashi da ya taba ci wa jiharsa. Igbinedion ya yi amfani da wannan kudin, ya biya bashinsa.

Source: Legit.ng

Online view pixel