‘Dan takarar Jam’iyyar YPP ya sallama, ya taya Farfesa Soludo murna, yace ba zai je kotu ba

‘Dan takarar Jam’iyyar YPP ya sallama, ya taya Farfesa Soludo murna, yace ba zai je kotu ba

  • Dan takarar jam’iyyar Young Progressive Party ya fitar da jawabi a game da zaben jihar Anambra.
  • Sanata Ifeanyi Ubah ya kira Farfesa Charles Chukwuma Soludo a wayar salula, ya taya shi murna.
  • Duk da ba haka ya so ba, Ifeanyi Ubah yace ba zai kalubalanci Jam’iyyar APGA da INEC a kotu ba.

Anambra - ‘Dan takarar jam’iyyar Young Progressive Party a zaben gwamnan Anambra, Ifeanyi Ubah, ya rungumi kaddara, yace bai da niyyar zuwa kotu.

Jaridar Punch ta rahoto Ifeanyi Ubah yana cewa ba zai kalubalanci sakamakon zaben da ya sha kashi a hannun ‘dan takarar jam’iyyar APGA a gaban kotu ba.

Sanatan na Anambra ta kudu a majalisar dattawan Najeriya, yace tun tuni ya kira wanda ya yi nasara, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya taya shi murna.

Read also

Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna

A wani jawabi da Ifeanyi Ubah ya fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, 2021, ya bayyana cewa shi da magoya bayansa sun rungumi kaddarar ubangiji.

Sanata Uba yace ba haka ya so ba, duk da ya yi alfahari da irin kokarin magoya-bayansa a zaben.

‘Dan takarar Jam’iyyar YPP
Sanata Ifeanyi Ubah Hoto: dailypost.ng
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cikakken jawabin da Ifeanyi Ubah ya fitar

Daily Post ta kawo rahoton jawabin da Uba ya fitar mai taken: 'Sanata Ifeanyi Ubah ya taya Farfesa Charles Soludo murnar nasarar da ya samu a zabe.”

“Yanzu na nan na kira zababban gwamnan jiharmu; Charles Chukwuma Soludo domin taya shi murna a kan nasarar da ya samu a zaben da aka yi.”
“Kamar yadda Injila ya fada; ‘komai da dalili’. Cikin godiya da sallamawa yin Ubangiji nake yi maku jawabi bayan samun goyon bayanku a zaben gwamna.”

Read also

Zaben Anambra: Manya-manyan ‘Yan siyasa 5 da suka fi kowa cin ribar nasarar APGA

Ba haka muka so ba, amma ... - Uba

“Ba haka muka so ba bayan wahalar da muka sha. Duk da wasu sun nuna ba su ji dadi ba a dalilin matsalolin da aka samu a rumfunan zabe da-dama.”
“Amma duk da haka, saboda kishin jiharmu, ba tare da la’akari da sakamakon ba, ina alfahari da kokarin da muka yi duk matsin lambar jami’an tsaro.”
“Na amince da sakamakon, na taya Soludo murna Ya kamata in sanar da cewa ba zan kalubalanci sakamakon zaben da aka sanar a kotu ba.” - Uba

APGA da IPOB: Ra’ayin Aisha Yesufu

Aisha Yesufu ta yi magana game da zaben Anambra, inda tace mutanen Kudu maso gabas za su amfana a siyasance idan kungiyar IPOB ta hada-kai da APGA.

‘Yar gwagwarmayar tana so tsagerun na IPOB masu gwagwarmayar Biyafara su hadu da jam’iyyar APGA domin su samu ta-cewa a siyasance a Najeriya.

Read also

Zaben Anambra: Buhari ya taya Soludo murnar lashe zaben gwamnan Anambra

Source: Legit.ng

Online view pixel