Jigon Jam’iyya ya bayyana abin da ya sa APC ta sha kunya a zaben gwamnan Anambra

Jigon Jam’iyya ya bayyana abin da ya sa APC ta sha kunya a zaben gwamnan Anambra

  • Tsohon ‘dan takarar gwamnan jihar Imo, Uche Nwosu ya soki APC a kan zaben gwamnan Anambra.
  • Uche Nwosu yace APC ta jawowa kanta abin da ya faru a zaben, kuma dole sai an yi gyara kafin 2023.
  • ‘Dan siyasar ya zargi APC da watsi da shugabannin da suka reni jam’iyyar a yankin kudu maso gabas.

Abuja - Tsohon ‘dan takarar gwamnan jihar Imo a karkashin jam’iyyar APC, Uche Nwosu ya yi magana game da zaben da aka gudanar a jihar Anambra.

A ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021, Uche Nwosu ya zanta da ‘yan jarida a Abuja, inda yace APC ta jawowa kanta rashin nasara a zaben sabon gwamnan.

Daily Trust ta rahoto Uche Nwosu yana cewa jam’iyyar APC ta kuka da kanta a zaben da aka yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Ondo ya yi koyi da Gwamna El-Rufai, ya yi karin 120% a kudin makarantar Jami'a

Nwosu ya shaidawa manema labarai cewa rashin sakayyar APC yana cikin abubuwan da suka sa jam’iyyar ta gagara tabuka abin kirki a zaben na Anambra.

Zunubun APC shi ne ta jefar da iyayenta

‘Dan siyasar yake cewa jam’iyyar APC mai mulki ta saki layi daga tsarin da iyayen gidanta suka gina ta a kai, tayi watsi da su, ta fifita wasu sababbin shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, jagororin APC sun yi wa wadanda suka kafa ta butulci a kudu maso gabas, yace an damka rikon jam’iyya a kan wadanda suka zo kwanan nan.

Jam’iyyar APC
Buhari ya ba Andy Uba tutar APC Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Nwosu yace wadanda suke juya akalar APC a yau, ba su san irin gumurzun da aka sha wajen kafa jam’iyyar ba. Leadership ta fitar da wannan rahoton a dazu.

“Abin da yake faruwa da APC a kudu maso gabas, dalilin rashin halacci ne. Jam’iyyar tayi watsi da wadanda suka dage, suka kafa ta a yankin.” – Nwosu.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Bayani a kan ‘Dan takarar APC wanda ya taba yin Gwamna na kwana 17

“Sai suka rungumi sababbin shiga da ba su san yadda za su jawowa jam’iyyar mutane ba.”

Ya APC za ta gujewa rashin nasara a 2023?

Jaridar Vanguard ta rahoto tsohon ‘dan takarar gwamnan na Imo yana cewa idan APC tana so ta lashe zabe mai zuwa ba da magudi ba, sai ta gyara cikin gidanta.

Suruki kuma tsohon hadimin na Sanata Rochas Okorocha yace akwai bukatar APC ta sasanta da tsofaffin kusoshinta, a ba su ragama, ko a sha kashi a zaben 2023.

Ya ake ciki a zaben Anambra?

Kuna da labari cewa tsohon Gwamnan CBN, Farfesa Charles Soludo ya sha gaban Jam’iyyar APC, PDP da YPP a zaben sabon gwamnan da aka yi a jihar Anambra.

Idan aka tafi a haka, Farfesa Soludo zai lashe zaben domin ya yi wa ‘yan takarar jam'iyyun adawa nisa. Sanata Andy Uba na APC ya na bayan 'dan takarar PDP ne.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya caccaki APC: Duk APC babu na gari, jam'iyyar 'yan rashawa ce

Asali: Legit.ng

Online view pixel