Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

  • Jam'iyyar APC mai mulki a ƙasar nan ta dakatar da gangamin taron ta na jihar Oyo
  • A sanarwar da ta fitar ranar Asabar da safe, APC tace ya zama wajibi ta ɗauki wannan matakin saboda wasu bayanai da ta gano
  • Tuni dai shugaban kwamitin riƙo, gwamna Mai Mala Buni, ya umarci kwamitin da aka tura jihar ya dawo Abuja

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan ta sanar da dakatar da gangamin taronta dake gudana yau a jihar Oyo saboda karya dokoki.

Rahoton dailytrust ya bayyana cewa APC ta ɗauki wannan matakin ne bisa samun bayanai cewa, "An ƙirƙiri wasu takardun da suka shafi taron na ƙarya da wasu dokokin da aka saɓa."

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar, Mai Mala Buni, shine ya bada wannan umarnin na gaggawa.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren APC na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, wadda ya fitar ranar Asabar da safe.

Shugaban APC, Gwamna Mai Mala Buni
Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwan ta bayyana cewa dakatarwan ta zama wajibi domin tabbatar da sahihancin taron wanda zai zaɓo sabbin shugabannin jam'iyya a jihar Oyo.

Ba zamu lamurci maguɗi ba - APC

Sanarwan ta ƙara da cewa, jam'iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ba zata amince da duk wani maguɗi da cuta ba yayin gudanar da taron.

Punch ta rahoto wani sashin sanarwan yace:

"Ya zama wajibi mu dakatar da gangamin taron dake gudana a jihar Oyo, saboda bayanan da muka samu game da shirin maguɗin takardun zaɓen da za'a gudanar."
"Shugaban jam'iyya na ƙasa ya umarci kwamitin zaɓen jihar Oyo ya dawo sakateriyar jam'iyya ta ƙasa dake Abuja domin ɗaukar mataki na gaba."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Gangamin taron APC na jihohi na gudana yau

Jam'iyyar APC ta tabbatarwa magoya bayanta cewa jam'iyya zata yi iya bakin kokarinta wajen tabbatar da adalci a kowane lokaci.

APC na gudanar da babban taronta na jihohi yau Asabar, 16 ga watan Oktoba 2021 a faɗim jihohin ƙasar nan.

A wani labarin kuma Sabbin bayanai kan shirin tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, na sauya sheka zuwa APC

Rahotanni sun bayyana wasu dalilai da yasa har zuwa yanzun tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, bai koma APC ba gabanin 2023.

Majiya mai ƙarfi ta shaidawa Leadership cewa Kwankwaso na fatan tsira da mutuncinsa kuma ya kafa wa APC wasu sharuɗɗa na shiga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel