Da Dumi-Dumi: Mala Buni ya yi tsokaci kan batun tsige Sakataren APC na ƙasa

Da Dumi-Dumi: Mala Buni ya yi tsokaci kan batun tsige Sakataren APC na ƙasa

  • Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban APC na riko, Mai Mala Buni, ya gana da sakataren kwamitinsa, Sanata John Akpanudoedehe
  • Rahoto ya nuna cewa haɗuwan manyan kusoshin APCn na nufin cewa batun tsige Sakataren ba gaskiya bane
  • Jam'iyya mai mulki ta shiga ƙaƙaniyakayi lokacin da Buni ya tafi duba lafiya Dubai, amma da alamu ta fara shawo kan lamarin

Abuja - Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa, Gwamna Mala Buni na jihar Yobe, ya gana da Sakataren kwamitinsa, John Akpanudoedehe.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Buni ya gana da Sakataren ne domin yin watsi da takardar dake yawo cewa mambobin kwamitin sun tsige shi daga kujerarsa ta Sakatare.

Gwamna Buni
Da Dumi-Dumi: Mala Buni ya yi tsokaci kan batun tsige Sakataren APC na ƙasa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jam'iyyar APC ta shiga dambarwa a cikin gida lokacin da shugaban rikonta na ƙasa, Mala Buni, ya tafi haɗaɗɗiyar daular larabawa domin duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Sarki Ilori ya nada shahrarren lauya, Alimi Abdulrasaq, matsayin Matawallen Ilori

Bayan tafiyarsa ne aka ga gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya maye gurbinsa a matsayin shugaba kafin ya dawo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a wata fira da kafar watsa labarai ta Channels TV, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya ce shugaba Buhari ne ya yi umarni da canza Buni.

A cewar Malam El-Rufa'i, gwamnonin APC guda 19 sun goyi bayan tsige Buni da kuma maye gurbinsa da gwamna Bello, wanda haka ya haifar da ruɗani.

Duk da wata wasiƙa da ta bayyana ta nuna cewa Buni ya damƙa ragamar tafiyar da APC a hannun gwamna Bello, wata takarda ta bayyana cewa mambobin kwamitin riko sun kaɗa kuri'ar rashin amincewa da Sakatare.

Buhari ya goyi bayan Buni

Yayin da ake cikin haka ne, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gargaɗi mambobin APC su maida wukarsu kube, su bar Buni ya gudanar da babban taro na ƙasa dake tafe.

Kara karanta wannan

Dankwambo, Fayose, Wike da Aduda na kokarin jan ra'ayin Goje ya koma PDP

APC ta zaɓi ranar 26 ga watan Maris, 2022 a matsayin ranar da zata gudanar da gangamin taro na ƙasa waɓda za'a zaɓi shugabanni.

A wani labarin na daban kuma Dubun wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika

Hukumar yan sandan ƙasar nan, ranar Alhamis, ta sanar da kame wani gawurtaccen ɗan bindiga da wasu mutum 26.

A cewar yan sandan, mutumin mai suna Yellow Ashana, ya amsa cewa su ke addabar matafiya a hanyar Kaduna-Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel