Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana kujerar da zai nema a zaben 2023

Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana kujerar da zai nema a zaben 2023

  • Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya sanar da kudirinsa na neman takara a 2023 bayan kammala wa'adinsa na gwamna
  • Ortom ya kawo karshen jita-jitar da mutane ke yaɗa wa kan siyasarsa ta gaba, inda ya ayyana shiga takarar sanata
  • Gwamnan ya fara ziyarar neman shawari kan shiga takarar sanata mai wakiltar shiyya ta B daga jihar Benuwai

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya kawo karshen rade-raɗin da ake yaɗawa a kan siyasarsa da kuma inda ya nufa bayan kammala mulki a 2023.

A ƙarshen makon nan, gwamnan ya bayyana sha'awar neman kujerar Sanata mai wakiltar jihar Benuwai ta arewa-yamma a zaɓe na gaba.

Daily Trust ta tattaro cewa kujerar a yanzu haka tana hannun Emmanuel Orker Jev, wanda ake hasashen zai iya neman goyon bayan mazabarsa domin zarce wa.

Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom
Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana kujerar da zai nema a zaben 2023 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ortom ya bayyana shirinsa na kawar da Sanatan dake ci daga kujerar, ranar Asabar lokacin da ya nemi goyon bayan mutanen Nzorov, sarakuna da sauran shugabanni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin taron, gwamna Ortom ya shaida wa mutanen Nzorov cewa yanzun ya samu natsuwar zuciya na ya nemi Sanata mai wakiltar Zone B karkashin jam'iyyar PDP.

Ya mutanen suka ɗauki lamarin?

A takaitaccen jawabin Ortom, ya sanarwa shugabannin al'umma cewa ya natsu, kuma Allah ya tabbatar masa ya nemi kujerar sanata kuma ya nemi sahalewar su.

Da yake jawabi a madadin Sarakuna, Hamimin Nzorov, Chief Gwatse Akaahena, ya tabbatar wa gwamnan Goyon bayan sarakuna da yan siyasa, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Ya ce za su goyi bayan ɗan su dari bisa ɗari ya tafi ya nemi takarar dan majisar dattijai mai wakiltar Zone B.

A sanarwar da kakakin gwamnan ya fitar, gwamna Ortom zai cigaba da neman shawarin shugabannin PDP da sauran masu faɗa a ji na mazaɓar da ya fito.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya amince da fitar da makudan kudade na kwaso yan Najeriya daga Ukraine

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ware makudan kudade domin aikin dawo da yan Najeriya gida daga Ukraine.

Karamin minista a ma'aikatar harkokin waje, Zubairu Dada, ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel