Da Dumi-Dumi: Ba gudu ba ja da baya game da ranar taron APC na ƙasa, Gwamnonin APC

Da Dumi-Dumi: Ba gudu ba ja da baya game da ranar taron APC na ƙasa, Gwamnonin APC

  • Gwamnonin jam'iyyar APC sun bayyana cewa ranar da aka sanya na taron APC na ƙasa na nan daram ba canji
  • Shugaban gwamnonin kuma gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu ne ya faɗi haka bayan ganawa da shugaba Buhari a Aso Villa
  • Ya ce sun gana da Buhari ne domin taya shi murnan rattaba hannu kan sabon kundin zabe da nasarar APC a zabukan maye gurbi

Abuja - Gwamnonin jam'iyyar APC sun jaddada cewa ranar da aka sanya na babban taron jam'iyya na ƙasa na nan daram kuma ba gudu ba ja da baya.

Jam'iyyar APC ta saka ranar 26 ga watan Maris da muke ciki, 2022, a matsayin ranar da zata saɓi shugabanninta na ƙasa, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, shi ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan ganawa da Buhari a Aso Villa, Abuja.

Gwamnonin APC
Da Dumi-Dumi: Ba gudu ba ja da baya game da ranar taron APC na ƙasa, Gwamnonin APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamna Bagudu ya kuma musanta raɗe-raɗin da mutane ke yaɗa wa cewa an samu rarrabuwar kai tsakanin gwamnonin APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Biyo bayan jadawalin zaɓen 2023 da hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar, APC ta tsinci kanta cikin matsanancin hali da matsin lamba.

Me gwamnonin suka tattauna da Buhari?

Bagudu ya ce gwamnonin sun gana da shugaba Buhari ne domin yi masa murna bisa rattaɓa hannu kan sabon kundin dokokin zaɓe 2022.

Hakanan kuma ya ce sun taya shugaban ƙasa murna kan nasarorin da APC ta samu a wasu zabukan maye gurbi da aka gudanar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Gwamnonin da suka halarci gana wa da Buhari sun haɗa da, Kayode Fayemi (Ekiti), Aminu Masari (Katsina), Nasir El-Rufai (Kaduna), Abubakar Badaru (Jigawa), Yahaya Bello (Kogi).

Kara karanta wannan

An yi gaba an dawo baya: Buhari ya nemi a soke wani sashe na sabuwar dokar zabe da ya sanyawa hannu

Sauran sun haɗa da, Hope Uzodinma (Imo), Gboyega Oyetola (Osun), Dapo Abiodun (Ogun), Sani Bello (Niger), Umar Ganduje (Kano) da mataimakin gwamnan Anambra, Nkem Okeke.

A wani labarin kuma Majalisa ta yi watsi da kudurin kirkiro wa mata Kujeru na musamman, da kudirin VAT

Majalisar tarayya ta kaɗa kuri'ar kin amincewa da kudirin kirkiro wa mata kujeru na musamman da kudirin canza wa VAT wuri.

Majalisar wakilan tarayya da kuma majalisar dattawa duk ba su amince da kudirorin ba a zaman garambawul ga kundin mulki 1999.

Asali: Legit.ng

Online view pixel