Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

  • Jam'iyyyar APC a jihar Imo ta bayyana cewa babu wanda ya sace Uche Nwosu, doka ce ta yi aiki a kansa
  • Yan sanda sun kama Nwosu, wanda siriki ne ga tsohon gwamnan jihar, Rochas Okoroca, a cikin coci
  • Rikici na kara zafi tsakanin gwamnan Imo na yanzun, Hope Uzodinma da Sanata Okorocha

Imo - Jam'iyyar APC reshen jihar Imo ta bayyana cewa doka ce ta yi aiki akan Uche Nwosu, tsohon ɗan takarar gwamna a jihar, ba wai sace shi aka yi ba.

Daily Trust tace wannan na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin APC a Imo, Mista Cajetan Duke, kuma aka raba wa manema labarai a Owerri ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan sanda sun sako sirikin Sanata Okorocha da suka cafke

Duke yace doka ba ta ganin mutuncin kowa kuma duk wanda ya ki amsa kiran hukumar yan sanda, hakan ka iya sa a kama shi ta tsiya a ko ina yake.

Uche Nwosu
Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamnanta a wurin Ibada Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa APC a jihar Imo karkashin jagorancin MacDonald Ebere, ba zata lamurci duk wani shashanci da zai sa gwamna Hope Uzodinma ya gaza shawo kan halin rashin tsaro a Imo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku daina yaɗa jita-jita mara tushe

Ya kuma shawarci yan Najeriya, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta, su daina yaɗa jita-jita mara tushe da wani ya kirkira domin sukar gwamna da jihar Imo baki ɗaya.

Yace:

"APC na goyon bayan gwamna da gwamnatin Imo bisa kokarin dawo da zaman lafiya da aminci da kuma cigaban tattalin arzikin a jihar mu."
"A jam'iyyance muna shawartan yan Najeriya su guji faɗawa cikin wani makirci da aka kirkira domin sukar gwamna Uzodinma."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da mota dauke da fasinjojinta ta fada magudanar ruwa

Okorocha ya caccaki gwamnan Imo

A ranar Lahadi, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya zargi gwamnan mai ci da hannu a kama Nwosu, wanda yake siriki a wurinsa.

Kazalika ya bayyana cewa yan sandan sun cafke sirikin nasa ne bisa umarnin shugabansu, Sufeta Janar na yan sandan ƙasar nan, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Malami ya bayyana yadda Buhari ya ceci ƙasar nan daga kifewa a bayan hawa kan mulki a 2015

Malami yace shugaba Buhari ya yi abin da ba kasafai shugabanni ke iya yi ba cikin shekara ɗaya da hawansa karagar mulki.

Ministan yace Buhari ya samu ƙasar nan tana tangal-tangal, kuma ya ceto ta daga kifewar tattalin arziki, wanda ka iya watsa kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel