Da Dumi-Dumi: APC ta sanar da ranar babban taron matan jam'iyya na ƙasa

Da Dumi-Dumi: APC ta sanar da ranar babban taron matan jam'iyya na ƙasa

  • APC ta zabi ranakun 16 da kuma 17 ga watan Fabrairu, 2022 a matsayin ranar babban taron matan jam'iyya na ƙasa
  • Shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mala Buni, ya amince da kafa kwamitoci 8 da zasu tabbatar da taron ya gudana cikin nasara
  • Ana sa ran uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, ce zata jagoranci taron, wanda ya kunshi mata daga jihohi 36 da Abuja

Abuja - Babban taron matan jam'iyyar APC na ƙasa zai gudana tsakanin ranakun 16 da 17 ga watan Janairu, na shekara mai kamawa 2022, kamar yadda Daiytrust ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Honorabul Stella Erhuvwu Okotete mamba mai wakiltar mata a kwamitin rikon kwarya na APC.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Sanarwan wacce aka fitar ranar Talata, ta ƙara da cewa uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ita ce shugaban taro, kuma ita zata bude taron.

Jam'iyyar APC
Da Dumi-Dumi: APC ta sanar da ranar babban taron matan jam'iyya na ƙasa Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Shugaban kwamitin CECPC, gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya amince da kafa kwamitoci 8 domin tabbatar taron ya gudana cikin nasara.

Waɗan ne kwamitoci APC ta kafa?

Kwamitocin sun haɗa da kwamitin shirye-shirye bisa jagorancin karamar ministan Abuja, Ramatu Tijani Aliyu, da mataimakiyarta, Doris Uboh-Ogunkoya da kuma Fatima Zarah Umar a matsayin sakatare.

Kwamitin kudi na da shugaba, ministan Zainab Ahmed, da kuma mataimakiyar gwamnan Ogun, Doris Uboh-Ogunkoya, a matsayin mataimakiyar shugaba da sakatariya, Irene Idabo.

Sai kwamitin tuntuba da jawo ra'ayin mata, wanda ya kunshi baki ɗaya shugabannin mata na jihohin ƙasar nan, Iman Sulaiman ce shugaba da mataimakiyar shugaba, Vivian Ere, da sakatariya, Ginika Tor William.

Kara karanta wannan

Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Ganduje ya kaiwa Kwankwaso bisa rasuwar kaninsa

Shugabar hukumar yan Najeriya dake kasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ita zata jagoranci kwamitin labarai da hulda da jama'a.

Sauran kwamitocin sun haɗa da kwamitin walwala da jin daɗi, kwamitin tsaro, kwamitin taro da tsara wurin taro, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Taron matan APC na tattara mata daga jihohin 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, domin tattauwa rawar da mata za su iya taka wa a ƙasa, cigaban jam'iyya da tattalin arzikin kasa.

A wani labarin na daban kuma Ana tsaka da jita-jitar tana da ciki Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi hutu sai baba ta gani

Mai dakin shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta baiwa ma'aikatan ofishinta hutu har sai baba ta gani.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke yaɗa jita-jitar cewa ko matar shugaban tana da juna biyu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel