Yahaya Bello: Marasa godiyan Allah ne kaɗai ba su yi wa Buhari godiya

Yahaya Bello: Marasa godiyan Allah ne kaɗai ba su yi wa Buhari godiya

  • Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce marasa godiyan Allah ne kadai ba su yi wa Buhari godiya bisa sadaukarwarsa
  • Gwamna Bello ya yi wannan jawabin ne yayin da wata tawaga daga Daura da sauran sassan Katsina ta kai masa ziyara a ofishinsa
  • Bello da ke neman maye gurbin Shugaba Buhari idan wa'adinsa ta kare ya ce Buhari ne kadai shugaban kasa da bashi da kadarori a kasashen waje

Jihar Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya jadada niyyarsa na zama magajin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari idan wa'adinsa ya kare a shekarar 2023.

Jaridar The Punch ta rahoto ya bayyana cewa marasa godiyan Allah ne kadai ba za su yaba da irin sadaukarwar da shugaban kasan ke yi ba don ganin Nigeria ta cigaba da zama kasa daya.

Read also

Bayan ganawa da Buhari, Tinubu ya bayyana abinda suka tattauna a kai

Yahaya Bello: Marasa godiyan Allah ne kaɗai ba su yi wa Buhari godiya
Marasa godiyan Allah ne kaɗai ba su yi wa Buhari godiya, Yahaya Bello. Hoto: The Nation
Source: Facebook

Gwamnan ya ce Buhari ne kadai shugaban kasar da ba shi da gidaje a kasashen waje ko asusun banki, sai dai shanunsa kawai kamar yadda ta zo a ruwayar ta The Punch.

Bello ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tarbar masu sarautun gargajiya, shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki daga Daura da wasu sassan Katsina da suka kai masa ziyara a ofishinsa.

Gwamnan ya ce abin da shugaban kasa ke bukata shine yan Nigeria da magoya bayansa su bashi hadin kai ya yi nasara.

Ya ce:

"Mara godiyan Allah ne kawai ba zai yaba da abin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kuma ya ke cigaba da yi wa kasar nan ba.
"A tarihi, shugaba Buhari ya dade yana sadaukar da kansa kuma har yanzu yana sadaukarwa domin hadin kai, tsaro, cigaba da 'yantar da kasar nan tun lokacin mulkin soja da ma yanzu a matsayin faran hula.

Read also

Ka hanzarta ceto nagartar ka, wadanda ka yarda da su ke batar da kai, Dalung ga Buhari

"Shine kadai shugaban kasar da ba shi da asusun ajiyar kudi a kasar waje, ko gidaje ko kamfanoni, illa shanunsa kawai. Ko lokacin da ya ke jinya, yana yi wa Nigeria fatan alheri."

Ya cigaba da cewa:

"A kalla, abinda za mu iya masa ko a bayyane ko a boye shine mu bashi goyon baya don ganin ya yi nasara. Don haka, duk abin da muke yi a yau don ganin ya yi nasara ne."

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

A wani rahoton kun ji cewa Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.

Read also

2023: Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso

Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.

Source: Legit

Online view pixel