Ramat: Zanga Zanga Ta Barke a Majalisa don Neman Tabbatar da Nadin Shugaban NERC

Ramat: Zanga Zanga Ta Barke a Majalisa don Neman Tabbatar da Nadin Shugaban NERC

  • Ana ci gaba da kai ruwa rana kan batun tabbatar da Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da lantarki ta Najeriya (NERC)
  • Wasu masu zanga-zanga sun gaji da jira inda suka dira majalisar dattawa don nuna fushinsu kan jinkirin da ake ci gaba da yi
  • Masu zanga-zangar sun sanar da majalisar illar rashin tabbatar da Ramat a shugabancin hukumar NERC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wasu daga cikin ‘yan asalin Jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Talata a harabar majalisar dokoki ta kasa

Mutanen dai sun gudanar da zanga-zangar ne don neman majalisar dattawa gaggauta tantancewa da tabbatar da Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da lantarki ta Najeriya (NERC).

An yi zanga-zanga kan Injiniya Ramat
Masu zanga-zanga da Injiniya Abdullahi Garba Ramat Hoto: @Jarmari01
Source: Twitter

An yi zanga-zanga kan nadin Ramat

Jaridar Daily Trust ta ce masu zanga-zangar, waɗanda suka iso a motocin Kano Line da wasu manyan motoci, sun rike fastoci da allunan da ke dauke da rubuce-rubuce.

Kara karanta wannan

Malamai sun fadawa Tinubu hanyar magance rashin tsaro da zafafan addu'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin rubuce-rubucen na cewa, “A girmama zabin Shugaba Tinubu", “Akpabio da Barau su daina raina Shugaba Tinubu,” da sauransu.

Sun bayyana cewa majalisar dattawa ta jinkirta tabbatar da Ramat duk da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya mika sunansa ga majalisa tun a ranar 7 ga Oktoba, 2025.

Abin da ya jawo jinkirin tabbatar da Ramat

Majalisar Dattawa ta bayyana cewa dalilin jinkirin tabbatar da Ramat shi ne korafe-korafe da dama da aka shigar kan nadin nasa.

Mai magana da yawun majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya karyata jita-jitar cewa shugabannin majalisar sun karɓi cin hanci na Dala miliyan 10 domin hana tabbatar da Ramat.

Matsayar masu zanga-zangar

Shugaban masu zanga-zangar, Ahmed I. Suleiman, yayin da yake jawabi ga manema labarai, ya ce babu wata hujja ta doka da za ta sa majalisar ta ki tabbatar da Ramat.

Kara karanta wannan

Dan Fodiyo: Majalisar shari'ar Musulunci ya roki Tinubu ya sauya shugaban INEC

Ramat ya samu magoya baya kan kin tabbatar da nadinsa
Masu zanga-zangar neman a tabbatar da nadin Injiniya Ramat Hoto: @Jarmari01
Source: Twitter

Ya ce kwamitin wutar lantarki na majalisar karkashin jagorancin Sanata Enyinnaya Abaribe ya riga ya tantance shi kuma ya ba da shawarar a tabbatar da shi, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Sun kuma mika wasiƙa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda suka mika kwafinta ga Shugaba Tinubu, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.

A cikin wasiƙar, masu zanga-zangar sun nemi majalisar ta gaggauta daukar mataki domin tabbatar da Ramat.

Sun bayyana cewa ci gaba da jinkiri yana iya iya lalata amincewar jama’a ga tsarin tabbatar da mukamai tare da hana kwararru sha’awar shiga aikin gwamnati.

Majalisar dattawa ta amince da nadin minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta tantance tare da amincewa da nadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Kingsley Udeh a matsayin minista.

Hakan na zuwa ne bayan bayan bukatar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar wa majalisar dattawa, inda ya nemi a tabbatar da Udeh a matsayin minista.

Kara karanta wannan

Majalisa ta karbi cin hancin $10m don kin tantance shugaban NERC? An ji gaskiyar zance

Mai girma Bola Tinubu Shugaba Tinubu ya nada Udeh ne biyo bayan murabus din tsohon ministan kimiyya, kirkire-kirkire da fasaha, Uche Nnaji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng