Hana Kudade ga Rivers: Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Halin da Ake Ciki
- Gwamnatin tarayya ta yi magana kan batun hana jihar Rivers kuɗaɗe daga asusunta duk wata
- Ofishin akanta janar na tarayya ya bayyana cewa za a sakarwa jihar kuɗaɗenta na watan Oktoba saɓanin rahotannin da ke cewa an riƙe su
- Daraktan yaɗa labarai na ofishin ya bayyana cewa za a saki kuɗaɗen ne saboda ɗaukaka ƙarar da aka yi a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi ƙarin haske kan batun daina bayar da kuɗaɗe ga jihar Rivers duk wata.
Gwamnatin tarayya ta ce ba ta daina bayar da kuɗaɗe ga jihar mai arziƙin man fetur ba saɓanin rahotannin da aka yaɗa a ranar Juma'a.
Gwamnatin tarayya za ta ba Rivers kuɗaɗe
Daraktan yaɗa labarai na ofishin akanta janar na tarayya, Mista Bawa Mokwa, ya bayyana hakan ga jaridar Tribune a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bawa Mokwa ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da bayar da kuɗaɗen na watan Oktoba waɗanda asusun gwamnatin tarayya ke rabawa jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya bayyana cewa jihar Rivers za ta samu na ta kuɗaɗen saboda ɗaukaka ƙarar da aka yi kan hukuncin kotun da ya hana a ba ta kuɗaɗe duk wata.
"Jihar Rivers za ta samu kuɗaɗen saboda ɗaukaka ƙarar da aka yi domin neman a dakatar da aiwatar da hukuncin."
- Bawa Mokwa
Kotu ta tanadi hukunci kan rikicin Rivers
A halin da ake ciki kuma, kotun ɗaukaka ƙara dake zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta tanadi hukunci a wasu ƙararraki biyar da suka biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ta yanke kan rikicin siyasar jihar Rivers.
Ɗaya daga cikin ƙararrakin dai ita ce ta adawa da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke wanda ya dakatar da babban bankin Najeriya (CBN) sakin kason jihar Rivers daga asusun gwamnatin tarayya.
Fubara ya magantu kan rikicin Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya yi magana kan rigimar siyasar da ke faruwa a jihar Rivers a Kudancin Najeriya.
Gwamna Fubara ya ce rigimar siyasar da ta bullo alheri ne ga jihar domin ta samar da yancin siyasa da bunƙasar tattalin arziki.
Asali: Legit.ng