Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Lakadawa Mahaifiyarta Duka a Jihar Anambra

Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Lakadawa Mahaifiyarta Duka a Jihar Anambra

  • Jami'an ƴan sanda sun yi caraf da matar da ta lakaɗawa dattijuwar mahaifiyarta dukan tsiya a jihar Anambra
  • An cafke matar ne bayan bayyanar bidiyonta tana cin zarafin dattijuwar mahaifiyarta lokacin da ta ke mata wanka
  • An yi Allah wadai da halin rashin darajar da matar ta nuna ga dattijuwar mahaifiyarta mai shekara 75 a duniya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Anambra - Ƴan sanda a jihar Anambra sun cafke wata mata mai suna Ukamaka Udugbo mai shekara 50 a duniya bisa lakaɗawa mahaifiyarta mai shekara 75 duka a yankin Abagana na ƙaramar hukumar Njikoka ta jihar.

Matar dai an ɗauke ta ne a cikin wani faifan bidiyo tana cin zarafin mahaifiyarta ta hanyar lakaɗa mata duka, cewar rahoton PM News.

'Yan sanda sun cafke matar da ta yi wa mahaifiyarta
Dattijuwar da aka lallasa da duka Hoto: Pmnews.com
Asali: UGC

DPO na ofishin ƴan sandan Abagana, SP Ifeanyi Umeh shi ne ya tabbatar da cafke matar da lokacin da wata ƙungiya mai zaman kanta '50-50 Action Group of the WomenAid Collective' (WACOL) ta ziyarce shi kan lamarin.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Gaskiya Kan Batun Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a Shekarar 2027

Umeh ya bayyana cewa sun samu labarin yadda matar ta ci zarafin mahaifiyarta mai suna Theresa Nwaokaka, wanda hakan ya sanya suka yi gaggawar zuwa cafko ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa da zarar sun kammala bincikensu za su tura da lamarin zuwa hedikwatar ƴan sanda ta birnin Awka.

An yi Allah wadai da halin matar

Ify Unachukwu, shugabar tawagar ta nuna godiyarta ga ƴan sanda kan yadda suka tunkari lamarin da gaggawa inda ta buƙaci da su tabbatar an ba lamarin muhimmanci domin hakan ya zama darasi ga saura.

Unachukwu ta bayyana lamarin a matsayin abun takaici ƴa ta lallasa dattijuwar mahaifiyarta inda ta yi kira ga matasa da su kiyayi yin koyi da wannan mummunar ɗabi'ar, rahoton The Punch ya tabbatar.

A cikin bidiyon an nuna Udugbo na lakaɗawa dattijuwar mahaifiyarra duka yayin da ta ke mata wanka a ƙauyen Obeagu Umudun cikin yankin Abagana.

Kara karanta wannan

An Sanya Dokar Bulala 40 Ko Tarar 10,000 Kan Duk Budurwar Da Ta Yi Shigar Banza a Wani Yankin Najeriya

Nwaokaka tana rayuwa ne a gidan ɗiyarta inda ta ke kula da ita.

'Yan Sanda Sun Cafke Likitan Bogi

A wani labarin kuma, ƴan sanda a jihar Jigawa sun cafke wani likitan bogi wanda ya daɗe yana cutar al'umma.

Likitan bogin ya buɗe wani babban asibiti ne a birnin Dutse na jihar inda yake gudanar da ayyukansa ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng