Jimami: Akalla Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya, 6 Sun Samu Raunuka a Mummunan Hatsarin Mota
- Hukumar FRSC reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane da dama a mummunar hatsarin da ya auku a hanyar Darazo
- Hatsarin ya auku a ranar Laraba 31 ga watan Mayu, da misalin karfe 01:32 na rana yayin da jami’an hukumar suka isa wurin bayan mintuna 10
- Mutanen da hatsarin ya afka da su, mutum 14 ne da suka hada da maza 5 da mata 6 sai kuma yara maza 2 da kuma yarinya mace daya
Jihar Bauchi – Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane takwas a wani mummunan hatsari da ya auku a jiyar Laraba 31 ga watan Mayu.
Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba 31 ga watan Mayu, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 01:32 yayin da jami’an hukumar suka isa wurin da misalin karfe 01:43 na rana.
Hatsarin ya faru akan hanyar Darazo zuwa Bauchi wanda ke da cunkoso kullum kusa da kauyen Shadarki, cewar Tribune.
Daya daga cikin motocin da hatsarin ya afka da su akwai farar Toyota Hilux mai lamba BPP 041 da kuma farar VolksWagen Golf 3 da ake amfani da ita daukar fasinja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yawan mutanen da hatsarin ya afka da su
Mutanen da hatsarin ya afka da su akalla sun kai 14 wanda suka hada da maza 5 da mata 6, sannan yara maza 2 da kuma yarinya mace daya, yayin da 6 daga ciki suka samu munanan raunuka.
Mutane takwas sun riga mu gidan gaskiya
Punch ta tattaro cewa akalla mutae takwas ne suka rasa rayukansu da suka hada da maza 2 da mata 3, sannan yara maza 2 da yarinya guda daya.
Mafi yawan raunukan da suka samu sun hada da kujewa da buguwar kai da kuma kaucewar kashi.
Hukumar ta yi gaggawan daukar wadanda abin ya rutsa dasu zuwa babban asibitin Darazo don basu kyakkyawan kulawa.
Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Hatsarin Mota a Bauchi
A wani labarin, an rasa rayuka da dama yayin da mutane takwas suka mutu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Bauchi
Hukumar FRSC ce ta tabbatar da haka inda ta ce hatsarin ya auku ne a kan hanyar Darazo zuwa Bauchi.
Asali: Legit.ng