Rundunar 'Yan Sandan Jihar Anambra Ta Sheke 'Yan Ta'addan IPOB Da Dama a Jihar

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Anambra Ta Sheke 'Yan Ta'addan IPOB Da Dama a Jihar

  • Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta samu nasarar halaka ƴan ta'addan haramtacciyar ƙungiyar IPOB mutum bakwai
  • Ƴan sandan sun halaka ƴan ta'addan ne a yayin wani sumame kashi biyu da ta kai kan ɓata garin
  • Rundunar ƴan sandan ta kuma samu nasarar kwato miyagun makamai a hannun ƴan ta'addan da aka tura inda ba a dawowa

Jihar Anambra - Rundunar ƴan sandan jihar Anambra, ta bayyana cewa jami'anta sun sheƙe mutum bakwai, mambobin ƙungiyar ta'addanci na Indigenous People of Biafra (IPOB)/Eastern Security Network (ESN) a jihar.

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa, an sheƙe mambobin haramtacciyar ƙungiyar ne, a wani sumame kashi biyu, da jami'an ƴan sanda suka kai a Ifite Ogbunike cikin ƙaramar hukumar Oyi, da Akwaihedi, cikin ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Atiku Ya Dira Da Tawagarsa Wajen Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa

Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta halaka 'yan ta'adda 7
Kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra, Echeng Echeng Hoto: Dailypost.com
Asali: UGC

A yayin tattaunawa da manema labarai, ranar Laraba, kwamishinan ƴan sandan jihar Echeng Echeng, ya ce rundunar ta yi aiki ne da bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta'addan a cikin ƙananan hukumomin biyu.

Ya bayyana cewa jami'an rundunar rapid response squad (RRS), Akwuzu, sun farmaki wani sansanin ESN a ƙaramar hukuma Oyi, lokacin da su ke ƙoƙarin ƙwato wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa jami'an tsaron sun halaka biyu daga cikin ƴan ta'addan, sannan suka ƙwato wata mota baƙa ƙirar Lexus SUV, tare da kayan ƴan sanda da na sojoji, cewar rahoton Tribune.

Echeng ya ce farmakin na biyu, ya auku ne lokacin da jami'an rundunar suka yi arangama da tawagar ƴan ta'addan akan babura suna kan hanyar su ta zuwa kai hare-hare a Anambra.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Jami'an Tsaro Masu Aikata Fashi Da Makami

Kwamishinan ya ce ƴan sandan sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan, inda suka sheƙe su gaba ɗaya. Ƴan sandan sun kuma kwato manyan makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK47 guda huɗu, harsasai guda bakwai, layoyi da dai sauransu.

IPOB Ta Shiga Jerin Kungiyoyin Yan Ta'adda 10 Mafi Hatsari a Duniya

A wani labarin na daban kuma, an jero sunan ƙungiyar IPOB, a cikin ƙungiyoyi mafi hatsari a duniya.

Ƙungiyar IPOB ta daɗe tana kai hare-hare kan jami'an tsaro da gine-ginen gwamnati a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng