Shugaba Buhari Ya Yi sabbin Naɗe-Naɗe Manya Watanni 2 Gabanin Ya Sauka

Shugaba Buhari Ya Yi sabbin Naɗe-Naɗe Manya Watanni 2 Gabanin Ya Sauka

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa sabbin manyan Sakatarori 6 a ɓangaren ma'aikatan gwamnatin tarayya
  • Wannan naɗin na Buhari na zuwa ne watanni biyu gabanin ya miƙa mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu
  • A ranar 29 ga watan Mayu, 2023, tsohon gwamnan Legas zai karbi mulkin Najeriya bayan nasarar da Allah ya ba shi a zaɓe

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ƙara sabbin naɗe-naɗe a bangaren ma'aikatan gwamnatin tarayyan Najeriya.

Shugabar ma'aikatan tarayya (HoCSF), Dakta Folasade Yemi-Esan, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, 29 ga watan Maris, 2023.

Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari Hoto: Presidency
Asali: UGC

Ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya amince da naɗin sabbin manyan Sakatarori guda shida, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jerin sunayensu

Sabbin manyan Sakatarorin da shugaban kasan ya naɗa sun haɗa da; Mahmud Adam Kambari daga jihar Borno; Esuabana Nko Asanya, daga jihar Kuros Riba da Lamuwa Adam Ibrahim daga jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Gombe: Fitaccen Basarake Mai Martaba Ya Rasa Mutum 2 a Cikin Iyalansa, Sun Rasu a Haɗari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran su ne; Yakubu Adam Kofar-Mata daga jihar Kano; Oloruntoba Olufemi Michael daga jihar Ogun; da kuma Richard P. Pheelangwah, daga jihar Taraba.

Sanarwan naɗin manyan Sakatarorin na ɗauke da sa hannun Darektan sashin sadarwa na ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Mallam Mohammed Abdullahi Ahmed.

Ya ce nan gaba a lokacin da ya dace za'a sanar da ranar rantsar da sabbin manyan Sakatarorin da kuma ma'aikatun da aka tura su, kamar yadda Dailypost ta rahoto.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan ci gaban na zuwa ne watanni buyu kacal gabanin karewar wa'adin mulkin Buhari da miƙa wa zababben shugaban kasa madafun iko.

A ranar 29 ga watan Mayu, 2023, za'a rantsar da shugaban kasa mai jiran gado, Tinubu, wanda ya samu nasara a zaben da INEC ta gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Karin Shekara: Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Ya Aike da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya Kafin Hawa Mulki

Canjin kudi ya yi tasiri kan yan bindiga da masu garkuwa - Ngige

A wani labarin kuma Ministan kwadugo ya bayyana tasirin da tsarin sauya kudi ya yi kan yan bindigan daji da masu garkuwa da mutane.

Bayan haka ya ce tsarin ya taka wa yan siyasa masu sayen ƙuri'u birki amma yanzun CBN ya ɗauki matakin tsamo yan Najeriya daga ƙunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262