Tinubu Ya Lashe Zabe a Karamar Hukumar Su Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

Tinubu Ya Lashe Zabe a Karamar Hukumar Su Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya lashe zabe a karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa, karamar hukumar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

A cewar sakamakon zaben da baturen zabe, Farfesa Joy Ikeke ya sanar, Tinubu ya samu kuri’u 8444, inda ya banke Peter Obi na Labour mai kuri’u 6721.

Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 6362 a karamar hukumar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A gefe guda, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya samu kuri’u 47.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel