Zaben 2023: Tsohon Gwamna Yari Ya Lashe Zaben Zamfara Ta Yamma

Zaben 2023: Tsohon Gwamna Yari Ya Lashe Zaben Zamfara Ta Yamma

Zamfara - An ayyana tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Zamfara ta Yamma a zaben da aka kammala a ranar Asabar 25 da watan Fabrairu, Channels ta rahoto.

Jami'in tattara sakamakon zabe na Zamfara ta Yamma, Farfesa Rufus Teniola na Jami'ar Tarayya ta Gusau, ya ayyana dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Abdulaziz Yari a matsayin wanda ya yi nasara.

Abdulaziz Yari
Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari yana magana da manema labarai. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Teniola ya ce Yari ya yi nasara da kuri'u 147,346 inda ya kayar da abokin fafatawarsa Bello S. Fagon na jam'iyyar Peoples Democratic Party wanda ya samu kuri'u 55,83.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sakamakon da aka kidaya, dan takarar jam'iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) ya samu kuri'u 363, yayin da dan takarar jam'iyyar Labour ya samu kuri'u 111.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ahmed Lawan Ya Sake Lashe Zaben Sanata a Yobe

Akwai kananan hukumomi shida a mazabar da suka hada da Gummi, Bukkuyum, Anka, Talata, Mafara, Maradun da Bakura.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel