Kotu Ta Haramtawa Abduljalil Ɓalewa Bayyana Kansa A Matsayin Dan Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa

Kotu Ta Haramtawa Abduljalil Ɓalewa Bayyana Kansa A Matsayin Dan Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa

  • Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana Dr Abduljalil cigaba da kiran kansa dan marigayi Tafawa Balewa
  • Hakan na zuwa ne bayan da yayan marigayi Balewa, Mukhtar, Saddik da Umar suka yi kararsa a kotu
  • Alkalin ya ce wadanda suka gabatar da karar sun nuna hujjar cewa Abduljalil ba dan uwansu bane, shi kuma ya gaza nuna hujjar zamansa dan Balewa

FCT, Abuja - Babban kotun tarayya na Abuja ta hana Abduljalil Balewa daga cigaba da kiran kasan dan marigayi firaiministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa, rahoton Daily Trust.

Mukhtar, Saddik da Umar, yaran marigayin firimiyan ne suka shigar da kara a gaban mai shari'a Peter Kekemeke, suna ikirarin cewa Mr Abduljalil da dan uwansu bane.

Tafawa Balewa
Kotu Ta Hana Abduljalil Ɓalewa Bayyana Kansa A Matsayin Dan Marigayi Firaminista. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Da ya ke yanke hukuncin a karar mai lamba FCT/HC/CV/956/2015, Kekemeke ya ce wadanda suka shigar da karar sun gamsar da kotu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce sun gabatar da hujoji a kotu biyo bayan karar da suka shigar.

Alkalin ya ce wanda aka yi karar, Mr Abduljalil, bai iya gabatar da hujjar cewa shi dan marigayin firaiministan bane, rahoton Vanguard.

Alkalin ya ce:

"Babu hujja da ke nuna cewa wanda ake zargin dan marigayi firaiminista ne ko inda aka haife shi. Babu hujja da ke nuna akwai aure tsakanin mahaifiyarsa da marigayin firaiministan.
"A gani na wadanda suka shigar da karar sun gabatar da gamsassun hujoji a gaban kotu."

Don haka an yanke hukunci an bawa wadanda suka shigar da kara gaskiya cewa wanda aka yi karar ba dan marigayi firaiministan bane, in ji alkalin.

Kotu ta hana wanda aka yi karar ya dena kiran kansa dan Sir Abubakar Tafawa Balewa

Alkali ya cigaba da cewa:

"Kotun ta bada umurnin hana wanda aka yi karar ya dena kiran kansa ko wakilansa ko bayinsa kiransa da, ko jika ko dangin Sir Balewa."

Alkalin ya kara da cewa:

"Bugu da kari, an bukaci wanda aka yi karar ya bada hakuri a jarida da kafafen watsa labarai cewa shi da ne ko jikan marigayi firaiminista. Kuma an ce ya biya N250,000 a matsayin tarar ikirarin da ya yi."

Kotu ta kori karar da aka shigar na neman haramtawa Tinubu takarar 2023

Kun ji cewa babban kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar na kalubalantar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu daga yin takarar a 2023.

Bayo Onanuga, direktan watsa labarai na kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC ne ya tabbatar da hukuncin kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel