Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Ya Ɗauki Mataki Kan Umarnin Kotu Ta Kulle Shi.
- Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, yace tuni ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Kotu ta yanke na tura shi gidan Yari
- Babbar Kotun Abuja ta umarci sufetan 'yan sanda na ƙasa ya tabbatar an garkame Bawa a gidan Yarin Kuje kan laifin rashin biyayya
- Alƙalin Kotun mai shari'a Chizoba Oji, yace Bawa ya yi fatali da umarnin da Kotu ta baiwa EFCC tun watan Nuwamba, 2018
Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, yace ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Kotu ta yanke na tsare shi a gidan Yari.
Bawa ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyim manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
"Mun ɗaukaka ƙara kan hukuncin tuntuni, saboda haka zamu bar doka ta yi aikinta," inji shugaban EFCC.
Meyasa Kotu ta umarci a tsare Bawa a gidan Yari?
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda wata Babbar Kotun Abuja ta umarci a iza ƙeyar Bawa zuwa gidan gyaran hali bisa gazawar hukumarsa na bin umarnin Kotu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Alƙalin Kotun mai shari'a Chizoba Oji, ya umarci Sufetan Janar na 'yan sandan Ƙasar nan, ya tabbatar an kai Bawa gidan Yari bisa laifin rashin biyayya.
Alkalin ya ɗauki wannan matakin ne yayin yanke hukunci kan bukatar da Adeniyi Ojuawo, air vice marshal mai ritaya ya shigar gabanta kan gwamnatin tarayya.
A rahoton Dailytrust, Mista Oji yace Bawa ya raina umarnin da Kotun ta ba shi bayan ƙin maida Mota ƙirar Range Rover da kuma kuɗi kimanin Miliyan N40m ga Ojuawo.
"Sakamakon ƙin bin umarnin wannan Kotu da ya ci gaba da yi, ya kamata a tsare shi a gidan Yarin Kuje kan rashin biyayya ga umarnin da wannam Kotun ta bayar ranar 21 ga watan Nuwamba, 2018 har zuwa lokacin da ya bi umarnin."
Jami’an EFCC Sun Dura Jihar Jigawa, Sun Kame Tsohon Kwamishinan Gwamna Badaru
A wani labarin kuma dakarun hukumar EFCC sun kai mamaya jihar Jigawa inda suka yi ram da tsohon Kwamishinan Badaru
Bayan kama shi, Jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin atziki ta'adi sun tasa ƙeyar tsohon Kwamishinan, Aminu Ahmed Kanta zuwa babban Ofishinsu na Abuja.
Mista Kanta, wanda ya rike kwamishinan kananan hukumomi a jihar Jigawa, jigo ne a APC kuma ɗan takarar majalisar wakilan tarayya a zaɓe mai zuwa.
Asali: Legit.ng