NDLEA Ta Bankado Kudi N20bn Cikin Asusun Banki 103 Mallakin Wani Shahrarren Dan Kasuwa a Legas

NDLEA Ta Bankado Kudi N20bn Cikin Asusun Banki 103 Mallakin Wani Shahrarren Dan Kasuwa a Legas

  • Hukumar hana fatauci da ta'amuni da muggan kwayoyi ta bankado wasu makuden kudade a asusun bankin wani da suke zargi
  • An bankado kudi N20bn a asusunan banki 103 na Mutumin da NDLEA ke yiwa zargin ta'amuni da kwayoyi
  • Hukumar ta umurci bankunan da wadannan kudade ke ciki su daskarar da su har zuwa an kammala bincike

Legas - Hukumar hana fatauci da ta'amuni da muggan kwayoyi watau NDLEA ta gano kudi N20bn dake asusunan banki guda 103 mallakin wani shahrarren dan kasuwan Legas, Mallinson Ukatu.

Tuni hukumar ta gurfanar da attajirin gaban kotu kuma yana garkame a gidan yarin Ikoyi.

Hukumar tana zarginsa da wasu laifuka 23 tare da wasu kamfanoninsa guda shida.

Punch ta ruwaito cewa ya gurfana gaban babban kotun tarayya dake Abuja.

Mallinson
NDLEA Ta Bankado Kudi N20bn Cikin Asusun Banki 103 Mallakin Wani Shahrarren Dan Kasuwa a Legas Hoto: Afam Mallinson Emmanuel Ukatu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

NDLEA ta kwace dukiyoyinsa 25

Hukumar tuni ta samu dama daga wajen kotu na kwace wasu dukiyoyin Ukatu guda 25.

Ana zarginsa da shigo da kwayar Tramol Najeriya na kudi N3bn.

Hakazalika ana zarginsa da almundahanar kudi $260, 268.25 a Access Bank.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida