Zaɓen 2023: Sanusi II Ya Fada Wa Musulmin Najeriya Makamin Da Za Su Yi Amfani Da Shi Don Kawo Canji A Kasar
- Khalifa Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano na 14 ya bukaci yan Najeriya su dage da addu'a don samun shugabanni na gari a zaben shekarar 2023
- Sanusi ya kuma ce musulmin Najeriya ba su da wani makami da ya fi addu'a don haka ya bukaci su dage da addu'o'i su kuma zabi wadanda suka cancanta
- Tsohon shugaban babban bankin na Najeriya ya yi wannan jawabin ne wurin taron Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya, Nigeria a ranar Lahadi a Abuja
FCT Abuja - Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya bukaci yan Najeriya su yi addu'a sannan su zabi shugabanni da suka cancanta da za su magance rashin tsaro da sauran kallubalen da kasar ke fuskanta.
Daily Trust ta rahoto cewa ya yi wannan kiran ne wurin taron kwamitin zartarwa (NEC) na Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya, Nigeria, ranar Lahadi a Abuja.
Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya, wanda kuma shine shugaban kungiyar ya bukaci yan Najeriya su hada kai don cigaban kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanusi ya ce:
"Abin da muke bukata shine kara hadin kan yan darika da inganta mu'amullan mu da sauran musulmi da yan Najeriya kuma mu taka muhimmin rawa don gina kasa.
"Akwai bukatar mu yi addu'ar zaman lafiya a Najeriya kuma Allah ya bamu shugabanni wadanda suka cancanta kuma masu gaskiya da za su yi wa al'umma hidima, musamman yanzu da muke fuskantar zabe ga kuma rashin tsaro a kasar, ba mu da wani makami da ya fi addu'a a matsayin mu na musulmi."
Ya cigaba da cewa:
"Don haka, ina kira ga dukkan ku ku cigaba da addu'ar Allah ya bamu shugabanni na gari da za su kare mu daga sharrin makiyanmu."
2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta
A wani rahoton, Malam Muhammad Sanusi II ya bayyana sayen kuri’u a matsayin wani sharri da ya zama barazana ga tsarin siyasar kasar nan.
Daily Trust ta ce Mai martaba, Muhammad Sanusi II ya yi jawabi ne a wajen wani taro na musamman da cibiyar dakin karatun Olusegun Obasanjo ta shirya.
Muhammad Sanusi II ya na ganin sayen kuri’a yana kawo babban cikas wajen zaben shugabanni.
Asali: Legit.ng