Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni Shida, Ya Tura Sunayen Su Majalisa

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni Shida, Ya Tura Sunayen Su Majalisa

  • Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Muhammed, ya aike da sunayen sabbin kwamishinoni Shida ga majalisar dokoki
  • Gwamnan ya kuma tura sunayen wasu naɗe-naɗe biyu masu muhimmanci da suka haɗa da Audita Janar domin tantance su
  • Majalisar dokokin ta sanya ranar da zata tantance tare da tabbatar da mutanen da gwamnan ya aika mata

Bauchi - Ƙasa da watannin shida gabanin babban zaɓen 2023, gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya naɗa sabbin kwamishinoni Shida, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abdul Ahmad Burra, ya fitar kuma aka raba wa manema labarai ranar Talata.

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi.
Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni Shida, Ya Tura Sunayen Su Majalisa Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Ya ce gwamna Muhammed ya aike da takarda ɗauke da sunayen mutanen da Allah ya baiwa muƙamin ga majalisar dokoki domin tantance su da kuma tabbatar da su.

Kara karanta wannan

2023: Shura Ta Gindaya Wa Malam Shekarau Sharudda 5 Idan Zai Sauya Sheka Zuwa PDP

Burra ya bayyana sunayen sabbin kwamishinonin da suka haɗa da, Abdulkadir Ibrahim (Alkaleri LGA), Zainab Baban Takko (Bauchi LGA), Adamu Babayo Gabarin (Darazo LGA), da kuma Maryam Garba Bagel (Dass LGA).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran su ne; Dakta Sabiu Abdu Gwalabe (ƙaramar hukumar Katagum) da kuma Ahmed Aliyu Jalam (ƙaramar hukumar Dambam), kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sauran naɗe-naɗen da gwamnan ya yi

Haka nan kuma gwamnan ya buƙaci majalisa ta tantance tare da tabbatar da naɗin Mista Joshua Titus Sanga a matsayin Darakta Janar na hukumar Public Procurement Bureau.

Bugu da ƙari, Ƙauran Bauchi ya nemi mambobin majalisar su tantance da tabbatar da Sagir Abdullahi Muhammad a matsayin sabon Audita Janar na jiha.

Sanarwan ta ce majalisa ta ɗora alhakin tantance Sanga da Muhammad kan kwamitin kasafin kudi da asusun gwamnati kuma ta baiwa kwamitocin wa'adin mako biyu su kawo rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisu Biyu da Dubbannin Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Arewa

Mista Burra ya bayyana cewa majalisar dokokin ta sanya ranar 7 ga watan Satumba, 2022 domin tantancewa tare da tabbatar da sabbin kwamishinonin.

A wani labarin kuma Yan Daban PDP Sun Kai Farmaki Wurin Taron Da Aka Shirya Domin Atiku Abubakar

Wasu yan daba sun tarwatsa ɗakin taron da aka shirya domin tabbatar da goyon bayan Atiku Abubakar a jihar Ribas.

Wata ƙungiya ta shirya taro a garin Bori, ƙaramar hukumar Khana da Ribas da nufin bayyana wa duniya mubaya'arta ga Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262