Fitaccen 'dan siyasan arewa kuma kwamishina a gwamnatin APC ya riga mu gidan gaskiya

Fitaccen 'dan siyasan arewa kuma kwamishina a gwamnatin APC ya riga mu gidan gaskiya

  • Kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Jigawa, Honarabul Salisu Zakari, ya riga mu gidan gaskiya
  • Tsohon shugaban hukumar SUBEB ne kuma ya taba rike sakataren jam'iyyar APC kafin ya shiga majalisar zartarwa ta jihar Jigawa
  • Kamar yadda majiya daga iyalansa ta sanar, ya rasu a safiya Asabar yana da shekaru 60 sakamakon rashin lafiyar da yayi

Kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Jigawa, Honarabul Salisu Zakari, mai sarautar cigarin Hadejia, ya riga mu gidan gaskiya.

Zakari mai shekaru 60 a duniya ya kwanta dama a safiyar Asabar a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano bayan gajeriyar rashin lafiya.

Honarabul Zangina
Fitaccen 'dan siyasan arewa kuma kwamishina a gwamnatin APC ya riga mu gidan gaskiya. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Kafin rasuwarsa, mamba ne a majalisar zartarwa ta jihar Jigawa dake arewacin Najeriya karkashin Gwamna Muhammad Badaru, Leadership ta ruwaito.

Kafin a nada shi kwamishinan kuma mamba a majalisar zartarwa ta jihar, mamacin shi ne shugaban hukumar SUBEB ta jihar kuma tsohon sakataren jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda majiya daga iyalansa ta bayyana, za a yi jana'izarsa a ranar Asabar a fadar sarkin Hadejia a jihar Jigawa da karfe 11 na safe.

A daya bangaren, gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya mika sakon ta'aziyyarsa inda ya kwatanta marigayin da mutumin kirki wanda ya bautawa Jigawa da gaskiya tare da jajircewa.

Bidiyo: Budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta fallasa yadda matar mamacin ke yi masa barbaɗe a abinci

A wani labari na daban, wata budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta bayyana kalaman karshe na mamacin wanda tace da kanshi ya bayyana mata.

A wani bidiyo da @natnats41 ta saka a TikTok, budurwar ta haye mumbari kuma tayi jawabi ga masu makokin mutuwar.

Ta fara ne ta hanyar jero sunayen 'ya'yan mamacin sannan ta fallasa wacce take zargin ta halaka shi.

Kara karanta wannan

Wike Ya Gayyaci Jigon APC, Wamakko, Ya Kaddamar Da Ayyuka A Rivers

Budurwar da tayi ikirarin cewa ta kwashe kwanaki uku da mamacin inda ta tambaye shi abinda ya kai shi kwance kuma kai tsaye ya bayyana abinda ke niyyar aika shi barzahu.

Ta kara da bayyana cewa, mamacin mai suna Paul ya sanar da ita cewa matarsa ce take yi masa barbaden wasu abubuwa a cikin abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: