Majalisar Tarayya Ta Bayyana Abin da Zai Hana a Tunbuke Buhari Daga Karagar Mulki

Majalisar Tarayya Ta Bayyana Abin da Zai Hana a Tunbuke Buhari Daga Karagar Mulki

  • Benjamin Kalu yana ganin ba zai yiwu a iya kammala tsige Muhammadu Buhari nan da Mayu ba
  • Kakakin yake cewa duka abin da zai ragewa Majalisa ta tunbuke shugaban kasar watanni bakwai ne
  • Hon. Kalu yana da ra’ayin cewa akwai abubuwan lura kafin a soma batun canza shugaban kasa

Abuja - Benjamin Kalu wanda shi ne mai magana da yawun bakin majalisar wakilan tarayya ya zanta da Punch a kan batun tsige shugaban kasa.

A hirar da aka yi da Honarabul Benjamin Kalu, ya tabo batun rashin tsaro, ayyukan majalisa da yunkurin sauke Mai girma Muhammadu Buhari.

Hon. Kalu yake cewa akwai bukatar ayi hattara idan aka yi la’akari da Muhammadu Buhari ne ya samu 55.6% na duk kuri’un da aka kada a 2019.

APC tayi nasara a jihohi 19, ‘dan takaranta yayi galaba a jihohin Legas da Kano, baya ga haka ya samu kuri’u masu yawa a sauran jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

Asarar dukiyar gwamnati

Mai magana da yawun majalisar yace an kashe $6.24 a kan kowane mutum wajen shirya zaben 2019, ma’ana, an batar da N4, 430 a kan kowa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da INEC ta kashe wajen shirya zaben da ya wuce ya haura N180bn, saboda haka Kalu yake ganin an yi asara idan aka tunbuke shugaban kasa.

Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari Hoto: Buhari Sallau Online
Asali: Facebook

Dole ayi hattara - Kalu

“Akwai bukatar a bi a hankali a kan wannan batun domin ba abin wasa bane kamar yadda ake fada. Ana batun tsige lamba ta daya ne a kasa.”
“Muna maganar canza zabin mafi yawan ‘yan kasar nan da suka zabe shi ya zama shugaban kasa.”
“Idan aka kawo maganar tsige shugaba, wanda za a fara bayan watanni biyu, abin tambaya shi ne ‘yanzu muna Agusta, watanni nawa gare mu?’

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Watanni tara suka ragewa gwamnatin Buhari, daga ciki kuma akwai kusan watanni biyu da za a cinye kafin a kai ga fara yunkurin canza shugaban kasar.

Majalisa ta ba shugaban kasa makonni shida ya magance matsalar, Hon. Kawu yace idan aka cire watanni biyu daga cikin lokacin, watanni bakwai zai rage.

A takaice dai, Newsngr ta rahoto Kalu yana cewa lokacin da ake da shi ba zai isa ayi nasara ba.

Bata lokaci ne - Shehu Sani

An samu labari Sanata Shehu Sani ya jero abubuwan da za su hana a iya sauke Shugaban Najeriya, yace za a bata lokacin majalisa ne kurum a banza.

Kwamred Shehu Sani yace lokaci ya kure, saboda haka ya nemi Sanatocin PDP da ke Majalisa su karkata wajen ganin yadda za a kifar da Gwamnatin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel