Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Mutum Uku Da Ya Naɗa Sabbin Muƙamai

Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Mutum Uku Da Ya Naɗa Sabbin Muƙamai

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya baiwa Sabbin sakatarorin dindindin uku da ya naɗa rantsuwar fara aiki a Abuja
  • Buhari ya rantsar da sabbin Sakatarorin ne gabanin fara taron mako-mako na majalisar zartarwa FEC yau Laraba
  • Ministocin gwamnatin Buhari da sauran mambobin FEC sun halarci taron, wasu kuma sun shiga ne ta fasahar zamani

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci bai wa sabbin Sakatarorin dindindin uku da ya naɗa rantsuwar kama aiki da shiga Ofis a fadarsa da ke Abuja.

Shugaban ƙasan ya yi haka ne a ɗakin taron da ke fadar shugaban ƙasa gabanin fara taron majalisar zartarwa FEC na mako-mako yau Laraba.

Mai taimaka wa shugaban ta fannin kafafen sada zumunta, Buhari Sallau, ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Jihar Shugaban Ƙasa Ta Tara Manyan Malamai, An Yi Addu'a Ta Musamman

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Mutum Uku Da Ya Naɗa Sabbin Muƙamai Hoto: Buhari Sallau/facebook.
Asali: Facebook

Sabbin Sakatarorin Dindindin ɗin sune, Lydia Shehu Jafiya daga jahar Adamawa, Udom Okokon Ekenam, daga jahar Akwa Ibom da kuma Farouk Yusuf Yabo, daga jahar Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kammala rantsar da mutanen, shugaban ƙasa Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa na wannan makon.

Sabbin Sakatarori.
Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Mutum Uku Da Ya Naɗa Sabbin Muƙamai Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Mutum Uku Da Ya Naɗa Sabbin Muƙamai Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Taron FEC.
Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Mutum Uku Da Ya Naɗa Sabbin Muƙamai Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Ƙusoshin Gwamnati da suka halarci taron

Taron wanda ke gudana yanzu haka da muke kawo muku rahoto ya samu halartan Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma'aikata, Folasade Yemi-Esan, da mai ba da shawara kan tsaro, Babagana Monguno.

Ministocin da suka hallara sun haɗa da na ma'aikatar kuɗi, kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, Yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammed, da Ministan Abuja, Muhammed Bello.

Sauran sune: Ministocin ma'aikatun kasuwanci da zuba hannun jari, Otunba Niyi Adebayo, saadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Sheikh Isa Pantami, wutar lantarki, Abubakar Aliyu, Kwadugo da ayyukan yi, Chris Ngige, da kuma ma'aikatar jin kai, Sadiya Farouq.

Kara karanta wannan

Babbar matsala sabuwa ta kunno, Wasu Sanatocin APC sun goyi bayan tsige shugaba Buhari

Baki ɗaya sauran mambobin majalisar da basu samu halarta da kansu ba sun shiga taron ta hanyar amfani da fasahar zamani watau Virtually.

A wani labarin kuma kun ji cewa Jigon PDP Da Daruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kebbi

Jam'iyyar PDP ta gamu da sabon koma baya a yunkurinta na kwace mulkin jihar Kebbi daga hannun jam'iyyar APC a zaɓen 2023.

Jigon PDP a ƙaramar hukumar Maiyama, Alhaji Abubakar Kurun Kuku ne ya jagoranci masu sauya sheƙan zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262