Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Joe Ohiani a matsayin shugaban hukumar ICRC
- Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Mista Joe Ohiani a matsayin shugaban Hukumar ICRC
- Kwamitin Adamu Aliero ya bayar da shawarar tabbatar da Ohiani bayan tantance shi tare da yi masa tambayoyi wadanda ya bayar da gamsassun amsoshi
- Tun farko dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sunansa gaban majalisa domin ta tabbatar da shi a matsayin Darakta Janar na Hukumar Kula da Ayyukan More Rayuwa
Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da Joe Ohiani a matsayin shugaban Hukumar Kula da Ayyukan More Rayuwa ta ICRC.
Tabbatarwan da aka yiwa Ohiani ya biyo bayan la’akari da rahoton kwamitin majalisar dattawan kan ayyuka, Premium Times ta rahoto.
Da yake jawabi, shugaban kwamitin, Adamu Aliero, ya ce an yiwa Mista Ohiani tambayoyi a kan aikin ICRC, da kuma yadda zai yi amfani da ilimi da gogewarsa wajen inganta ayyukan hukumar.
Aliero ya sanar da takwarorinsa cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Wanda aka zaban ya mayar da martani cike da basira sannan ya bayar da gamsassun amsoshi ga duk tambayoyin da aka yi masa."
Kwamitin ya kuma bayar da shawarar cewa zabin shugaban kasar ya cancanci a tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar, bayan ya yi nazari tare da tantance shi da ya yi da kyau, rahoton Daily Post.
‘Yan Majalisa sun tono wanda Shugaban kasa ya ba mukami bai da shaidar karatun Firamare
A baya mun ji cewa a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni 2022, Majalisar dattawa ta gano cewa wanda ake so ya zama shugaban hukumar ICRC ta kasa yana da nakasa.
Rahoton da ya fito daga Vanguard ya tabbatar da cewa Joe Anekhu Ohiani bai da takardar kammala firamare domin bai karasa karatu ba, ya yi gaba.
Mista Joe Anekhu Ohiani ya tsaida karatun firamarensa ne a aji biyar, don haka bai da satifiket.
Kamar yadda ya fada da bakinsa Ohiani ya ce a aji biyar ya rubuta jarrabawar shiga sakandare, ya samu nasara, uzurin da Sanatocin sam ba su karba ba.
Asali: Legit.ng