Da duminsa: Bayan sa'o'i kadan da ganawa da Buhari, Sakatare janar na OPEC ya rasu
- Sakatare janar na Kungiyar Kasashe masu fitar da man fetur, Muhammad Sanusi Barkindo, ya riga mu gidan gaskiya
- Barkindo ya rasu a ranar Talata wurin karfe 11 na dare yayin da yake da shekaru 63 a dunya kamar yadda Mele Kyari ya sanar
- Barkindo shine tsohon GMD na NNPC na uku da ya rasu cikin shekaru biyu bayan Maikanti Baru da Joseph Dawha
Muhammad Sanusi Barkindo, sakataren janar na Kungiyar Kasashe masu fitar da man fetur, ya rasu.
Mele Kyari, manajan daraktan Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, ya bada sanarwar mutuwarsa a wallafarsa ta Twitter a sa'o'in farko na ranar Laraba.
Kyari yace ya rasu wurin karfe 11 na daren Talata, yana da shekaru 63 a duniya.
Ya kwatanta rasuwarsa da babban rashin ga iyalnsa, NNPC Najeriya, OPEC da duniya baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun yi rashin Dr Muhammad Sanusi Barkindo. Ya rasu wurin karfe 11 na daren jiya, 5 ga watan Yulin 2022. Babu shakka wannan babban rashi ne ga iyalansa, NNPC, kasarmu ta Najeriya, OPC da duniya baki daya," Kyari ya wallafa a Twitter.
“Za a sanar da shirin jana'iza nan babu dadewa."
Barkindo shi ne na uku a cikin tsofaffin GMD na NNPC da ya rasu a cikin shekaru biyu. Maikanti Baru ya rasu a watan Mayun 2020, sai Joseph Dawha ya rasu a watan Augustan 2020.
Allah Yayi wa Dr Ahmad Yakasai, MD na HML din 'Yan Sandan Najeriya, Rasuwa
A wani labari na daban, Allah ya yi wa Dr. Ahmad Garba Yakasai, manajan daraktan Cibiyar Gudanarwa ta Kiwon Lafiya ta 'Yan sandan Najeriya, rasuwa.
Kwararren likitan 'dan asalin jihar Kano, ya rasu ne sakamakon mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi a babban titin Damaturu, jihar Yobe.
Ya rasu a ranar Asabar, 18 ga watan Yunin 2022 kuma na yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a cikin garin Kano wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.
Asali: Legit.ng